Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Iran Zata YI Zama Na Musamman Kan Zanga-zangar Dake Faruwa


Masu zanga-zanga a Iran

A yau Lahadi aka shirya ‘yan Majalisun Iran zasu yi wani zama na musamman domin tattauna batun zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka fara tun ranar 28 ga watan Disamba, wadda ke ci gaba da wakana har ya zuwa yanzu.

Kafar labaran ISNA ta Iran ta rawaito cewa ana kyautata zaton ministan cikin gida da shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa da kuma shugaban majalisartsaro zasu halarci taron. Ajandar tattaunawar ta kunshi gano makasudin abin da ya haddasa zanga-zangar, da kuma irin taimakon da za a iya baiwa wadanda aka kama lokacin zanga-zangar a shari’ance.

Wasu ‘yan majalisa masu neman sauyi ne suka yi kiran ayi taron, a cewar gidan rediyon Liberty da kuma Radio Free Europe. A wata wasika, ‘yan majalisun sun kira da taimakawa wadanda aka Kaman a shari’ance, kuma sukayi Allah wa dai ga duk wani katsalandan daga kasashen waje kan zanga-zangar dake faruwa, suna masu ambaton Amurka musamman.

A mako mai zuwa ne shugaban Amurka Donald Trump zai yanke hukunci kan ko Amurka zata ci gaba da ‘dagawa Iran kafa kan yajejeniyar shekarar 2015 da aka kulla ta kasa da kasa kan shirin Nukilyar Iran. Wadda aka tsara duk kwanaki 120 sai an sabuntata. Trump na iya yanke shawarar kin sabuntata wanda hakan zai iya maido da takunkumin cinikayya da Amurka ta sawa Iran din.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG