Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Girgizar Kasa: Shugaba Buhari Ya Jajantawa Turkiyya Da Siriya Kuma Ya Yi Alkawarin Tallafi


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

A cikina wata sanarwar da Mai ba shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga gwamnatoci da al'ummar Turkiyya da Siriya.

Ya kuma jajantawa wadanda suka rasa 'yan uwa da abokan arziki a girgizar kasar da ta afku a garin Gaziantep da ke kudancin kasar Turkiyya.

Shugaban ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa, ya kuma ba da tabbacin cewa addu’o’i da tunanin ‘yan Nijeriya na tare da dimbin wadanda wannan mummunan bala’i da fargaba ya shafa.

A matsayinsa na aminin Turkiyya da Siriya, Shugaba Buhari ya ce Najeriya a shirye take ta ba da cikakken goyon bayan ta ta kowace hanya.

XS
SM
MD
LG