Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Ministocin Isra’ila Ta Amince Da Yarjejeniyar Daidaita Dangantaka Da UAE


Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar gyara dangantaka tsakanin kasar da Hadaddiyar Daular Larabawa da ake kira UAE a takaice.

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Litinin 12 ga watan Oktoba cewa shi da Yariman masarautar Abu Dhabi mai jiran gado, Mohammed bin Zayed Al Nahyan sun amince su gana nan ba da dadewa ba.

Ana sa ran majalisar dokokin Isra’ila za ta kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar a cikin wannan makon.

Netanyahu da Sheikh Mohammed sun yi magana ta wayar tarho kuma a sanarwar da kowannensu ya fitar a ranar Litinin, sun ce sun tattauna kan batutuwa da dama, ciki har da samar da zaman lafiya da hadin gwiwa a Gabas ta Tsakiya.

Isra’ila da UAE sun sanya hannu a yarjejeniyar da Amurka ta shiga Tsakani aka kulla a wani biki da aka yi a fadar White House a watan Satumba inda Isra’ila kuma ta sanya hannu a shigen irin yarjejeniyar da Bahrain.

UAE ce kasa ta 3 kuma kasar larabawa ta 4 da ta kulla irin wannan yarjejeniyar da Isra’ila, bayan Masar a shekarar 1979 da Jordan a shekarar 1994.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG