Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bahrain Ta Amince Da Isra'ila


Isra'ila da Bahrain

Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da sanarwar cewa Daular Bahrain ta amince da Isra’ila a matsayin kasa, biyo bayan irin wannan yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa a watan da ya gabata.

Wannan yarjejeniyar dai wata manuniya ce ta wani muhimmin sauyi a Gabas Ta Tsakiya, wadda ke kokarin kusanto da kasashen larabawa kusa da Isra’ila, a yayin da kuma ake kallon tana mai da Falasdinawa saniyar ware.

A cikin ofishinsa da ke fadar White House, Trump ya ce ya karbi bakuncin wani “kiran wayar tarho mai cike da tarihi” tsakanin Prime Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Sarki Ahmad Al Khalifa na Bahrai, inda shugabannin suka cimma matsayar cewa Bahrain “za ta daidaita dukkan dangantakar difilomasiyyar ta da Isra’ila.”

Trump ya bayyana wannan yunkurin a matsayin “muhimmin al’amari da zai karfafa zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.”

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Trump ya fadawa manema labarai da safiyar Juma’a cewa “babu wani kakkarfan martani akan kiyayyar da ke tattare da harin 11 ga watan Satumba da ya wuce wannan yarjejeniya da muke shirin fada muku.”

Da safiyar Juma’ar ne shugaban na Amurka ya tafi Shanksville ta jihar Pennsylvania, domin tunawa da shekaru 19 na harin ta’addanci na 11 ga watan Satumban shekara ta 2001.

Yarjejeniyar ta Bahrain ta biyo ne bayan “Yarjejeniyar Abraham” ta ranar 13 ga watan Agusta, wata yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Daular Larabawa na daidaita dangantakarsu.

A zaman wani sashe na yarjejeniyar, Prime Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince ya dakatar da shirinsa na fadada matsugunai a Gabar Teku. Fadar Shugaban Amurka ta White House ce za ta karbi bakuncin bikin rattaba hannu akan yarjejeniyar a farkon mako mai zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG