Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar mulkin soja ta kasar Masar, ta yiwa masu zanga zangar kashedi.


Masu zanga zangar a dandalin Tahrir na kasar Masar suka kama wasu maza da suka kai musu hari.

A wata sanarwar da kaukashan harshe da aka karanta ta gidan talibijin na kasar, da aka tsara da nufin shawo kan mutane, su daina tare ofisoshin gwamnati kamar yadda suka shirya. Wani wakilin Majalisar mulkin kasar Janaral Mohsen Al fangari ya yiwa masu kishin kasa kashedin cewa kada su kuskura su kaucewa zanga zangar lumana da suke yi, domin baiyana bukatunsu ko kuma su dauki wani mataki da ba zai zamewa kasar alheri ba

Wasu matasa a wani tanti a dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin Alkahira na kasar Masar, sunyi ta rera wata waka da aka yi a shekarun alif dari tara da hamsin, wadda kalamominta suke nuni da juyin juya halin da suka yi, suna masu fadin cewa suna son kasar Masar ta koma kamar abinda suke ganin martabar ta ta da.

A yayinda suke rera wannan waka, wasu mutane suna bi ta wurin bincike domin yin na’am da kiran da masu kishin kasa suka yi na yin wani baban gangamin nuna rashin amincewa

. Su dai mutane suna kukar cewa Majalisar mulkin soja ta kasar da kuma Prime Minista Eassam Sharaf basa daukan matakai cikin saurin daya kamata na kaddamar da sauye sauye da kuma yiwa jami’an tsohuwar gwamnati da jami’an tsaro shari’a ko kuma hukunta su.

A ranar litinin Prime Ministan kasar yayi alkawari yiwa Majalisar Ministocinsa garambawul kuma ya zuwa ranar lahadi zai nada sabbin gwamnoni. Yace zaiyi murabus idan bai cimma wannan buri ba. Daga baya gwamnati ta bada sanarwar cewa ta fara yiwa Majalisar ministoci garambawul a yayinda mataimakin Prime Minista yayi murabus, kuma tace za’a gudanar da tarurrruka domin yanke shawara akan wasu canje canjen da za’a kaddamar.

Haka kuma a jiya talata, wata kotun Masar ta yankewa tsohon Prime Minista da wasu tsaffin Ministoci hukuncin daurin kimamin shekaru goma a gidan yari, bayan da aka same su da laifin cin hanci. Su dai wadannan tsaffin jami’an sunyi aiki karkashin tsohuwar gwamnati Hosni Mubarak wanda shi kansa yake fuskantar caje cajen cin hanci da rashawa bayan da yayi murabus a watan fabrairu.

To amma ga mutane da suka yi cincinrindo a dandalin Tahrir suna ganin gwamnati tana tafiyar hawainiya kuma bata daukan matakai akan lokaci.Wani mutum mai suna Abdullahi Noufai, wanda shine direktan sadarwa na daya daga cikin kungiyoyin da suke zanga zangar nuna rashin amincewa mai suna April Sixth Movement. Ya fadawa muryar Amirka cewa yayi watani yana jin alkawuran da Prime Ministan kasar ke yi kamar na baya bayan nan. Yace lokaci yayi daya kamata a aiwatar a zahiri, ba fadi da fatar baki kurum ba

Yace wannan juyin juya hali ne daya yi farin jinni, ba juyin mulkin soja ba. Kuma yace zai ci gaba da kasancewa a dandalin Tahri har sai lokacinda shugabanin soja suka biya bukatun masu zanga zangar. Ba shi kadai ne keda wannan ra’ayi ba, akwai akalla daruruwan mutane wadanda suka kafa tantuna a dandalin.

Jiya talata aka samu hargitsi a dandalin lokacinda masu zanga zangar suka ce kimamin maza talatin dauke da wukake da kuma sanduna suka kai musu hari. Sun raunana mutane da dama, kafin masu zanga zangar suka fatattakai su. Ba’a dai tantance ko su wanene suka kai harin ba. A yayinda zaman tankiya ke karuwa a dandalin Tahrir da alama itama gwamnati ta fara gajiya da masu zanga zangar.

A wata sanarwar da kaukashan harshe da aka karanta ta gidan talibijin na kasar, da aka tsara da nufin shawo kan mutane, su daina tare ofisoshin gwamnati kamar yadda suka shirya. Wani wakilin Majalisar mulkin kasar Janaral Mohsen Al Fangari ya yiwa masu kishin kasa kashedin cewa kada su kuskura su kaucewa zanga zangar lumana da suke yi, domin baiyana bukatunsu ko kuma su dauki wani mataki da ba zai zamewa kasar alheri ba.

A yayinda yake sanye da rigarsa ta soja kuma yana nuna yatsa a lokacinda yake magana, janaral Al Fangari yace Majalisar mulkin soja zata sauka daga kan mulki bayan anyi zabe, da aka shirya yi wani lokaci a wannan shekara idan Allah ya yarda. Haka kuma yace majalisar ta dauki matakin tinkarar daya daga cikin bukatun masu zanga zangar.

Editar jaridar turanci ta Daily News Egypt, Rania Al Malky tace ta fahimci rashin hakurin masu zanga zangar akan wasu batutuwa, to amma tace ya kamata akan wasu batutuwa su ci gaba da yin hakuri. Tace idan ana batun yiwa jami’an yan sanda shari’a, masu zanga zangar suna da hujja. To amma tace idan ana batun bukatar cewa a hanzarta yin shari’ar, kuma idan har ana son ayi adalci. Tana ganin akwai bukatar mutane su kara yin hakuri. Al Malky tace gwamnati tana tafiyar hawaniya wajen kaddamar da sauye sauye, cikin watani biyar tun lokacinda ta karbe jan ragamar mulki, shi yasa mutane suke tababan yarda, jami’a zasu shika alkawuran da su ka yi.

XS
SM
MD
LG