Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Uganda ya yi kira da a fadada aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya


Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi kira da a fadada kamfe kan mayakan Somaliya da cewa, kasar tana barazana ga tattalin arzikin gabashin Afrika yayinda kuma take shigo da ayyukan ta’addanci a yankin.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi kira da a fadada kamfe kan mayakan Somaliya da cewa, kasar tana barazana ga tattalin arzikin gabashin Afrika yayinda kuma take shigo da ayyukan ta’addanci a yankin. A cikin sanarwar da aka buga a shafin shugaban kasar na duniya gizo, Mr. Musveni yace dakarun kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya tana bukatar kayan aiki ta sama da kuma teku domin shawo kan mayakan al-Shabab. Yace yana so ya fadada matakin da ake dauka ta doron kasa kawai. Sojojin kasar Uganda sune akasarin dakarun kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika dake marawa gwamnatin kasar Somaliya baya. Mr. Museveni ya bayyana haka ne yayinda ake cika shekara guda da tagwayen hare haren da aka kai Kampala babban birnin kasar da suka yi sanadin mutuwar mutane 76. Kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin kai hare haren a matsayin ramuwar gayya kan Somaliyawan da dakarun Kungiyar Tarayyar Afrika suka kashe.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG