Accessibility links

Majalisar Mulkin Wucin Gadi Ta Libya Ta Mika Mulki


Shugaban majalisar mulkin wucin gadi, Mustafa Abdel Jalil (dama) yana gaisawa da firayim ministan zamanin yaki,Mahmoud Jibril 8 Agusta 2012

Mustafa Abdel Jalil, shugaban majalisar mulki ta wucin gadin, ya mika ragamar mulki ga zababbiyar majalisar dokoki ta kasa daren laraba a Tripoli

Majalisar mulkin wucin gadi ta kasar Libya ta mika mulki cikin lumana ga majalisar dokokin kasar ta farko da aka taba zaba.

Mustafa Abdel Jalil, shugaban majalisar mulki ta wucin gadin, ya mika ragamar mulkin kasar ga mutum mafi yawan shekaru cikin zababbiyar majalisar, Mohammed Ali Salem, a wurin bukin da aka gudanar cikin daren laraba a wani hotel na birnin Tripoli.

Abdel Jalil yace daga yanzu, wannan majalisa wadda ake kira Babbar Majalisa ta Kasa, ita ce halaltacciyar wakiliyar al’ummar kasar Libya.

Majalisar da aka zaba ta kunshi kujeru 120 na masu zaman kansu da kuma wasu kujeru guda 80 da aka ware don jam’iyyu. Gungun jam’iyyu masu sassaucin ra’ayi dake goyon bayan firayim minista na lokacin yaki Mahmoud Jibril, sune suka fi taka rawa a zaben na watan da ya shige, inda suka samu kujeru 39.

A yanzu dai wannan majalisa mai wakilai 200 ita ce zata nada sabon shugabanta tare da yin jagorar kasar Libya zuwa ga cikakken zaben majalisar dokoki ta dindindin, a bayan an zana sabon daftarin tsarin mulki.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG