Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Na Neman Gudanar Da Ayyukansu Daga Gida


The U.S. Capitol

A yau Laraba wani kwamitin majalisar wakilan Amurka zai yi wani taro domin tattauna wani kuduri dake neman bai wa ‘yan majalisa damar wakilta wani ya jefa musu kuri’a, da kuma ba kwamitotci damar gudanar da taron tattaunawa daga wuraren da suke.

Matakin da aka gabatar zai ba ‘yan majalisar karin sassauci wajen gudanar da aikinsu a lokutan da aka samu barkewar annoba, kamar wannan lokacin na cutar coronavirus da ya sa aka dauki matakin hana taron mutane da yawn.

A cikin wannan lokacin, dan majalisa zai gabatar da wasika ya kuma fadi dan majalisar da zai kada masa kuri’a bayan an shata masa dokoki da ka’idodi.

Za a iya sauya wadannan tanade-tanaden a ko wane lokaci, kana magatakardan majalisar zai ci gaba da fitar da jerin sunayen ga jama’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG