Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Gwamnatinsa Na Kokarin Samar Da Karin Kayan Gwajin Coronavirus


Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa na aiki don samo karin kayan gwajin annobar cutar coronavirus a yayin da ‘yan majalisar dokokin kasar daga jami’yyun Republican da Democrat suka ce sun kusa cimma yarjejeniyar samar da karin kudaden tallafa wa kananan sana’o’i.

‘Yan jam’iyyar Democrat sun yi suka da kakkausan lafazi akan matakan Shugaban kasar na tunkarar annobar, musamman game da rashin samar da isassun kayan gwajin cutar, ta yadda za a iya gano mutanen da suke dauke da cutar kana a killace su, da kuma gano wadanda duk suka yi mu’amala da su.

A jiya Lahadi lokacin ganawa da manema labarai na fadar White House, Trump ya ce sun cimma matsaya da wani kamfanin kasar da ya karkata akalar ayyukansa zuwa samar da na’urar taimaka wa masu matsalar numfashi kimanin miliyan 10 a duk wata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG