Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Tsige Shugaba Donald Trump


Trump Impeachment
Trump Impeachment

Majalisar Wakilai a daren jiya Laraba ta tsige shugaba Donald Trump, inda ta zarge shi da yin amfani da mukaminsa na shugaban kasa ba bisa ka’ida ba domin taimakawa kan sa a siyasance, da kuma kawo cikas ga kokarin majalisa na binciken ayukan sa.

A zaben da ya kasance kusan na jam’iyya daya, majalisar mai rinjayen ‘yan Democrats, ta aminta da daftarori 2 na zarge-zargen tsige Trump, dan jam’iyyar Republican, da ya kasance shugaban Amurka na 3 da aka tsige a tarihin kasar mai shekaru 243.

Trump wanda ya bayyana yunkurin tsige shi a zaman shirme, ya kuma soki lamirin ‘yan Democrats akan yunkurin, a yanzu zai fuskanci shari’a a majalisar dattawa wani lokaci a watan Janairu.

To sai dai akwai yiwuwar majalisar dattawan mai rinjayen ‘yan Republican, ta wanke shi daga zarge-zargen, inda za ta baiwa masu zabe damar yanke hukuncin a kan makomar Trump, a yayin da yake neman zarcewa a wa’adin mulki na 2, a zaben da za’a gudanar a watan Nuwamba.

Fadar shugaban kasa ta White House ta fitar da sanarwa jim kadan bayan kada kuri’ar tsige Trump, inda ta ke cewa “Yau rana ce da aka aikata daya daga cikin lamurran siyasa mafi kunya a majalisar a tarihin kasar nan”.

Sanarwar ta bayyana matakin a matsayin abin kunya.Sanarwar ta ci gaba da cewa shugaba Trump na da yakinin cewa majalisar Dattawa za ta daidaita al’amura, ta tabbatar da doka da adalci da aka yi watsi da su a dukkan zaman tsigewar a majalisar wakilai, kuma tuni da shiryawa tunkarar mataki na gaba, in da yake da yakinin za’a wanke shi.

A cikin hirar sa da Grace Alheri Abdu, mai sharhi akan siyasar Amurka, Aminu El-Yakubu Lame, ya yi karin haske akan mataki na gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:15 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG