Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisun Dokokin Amurka da Shirin Nukiliyar Iran


Taron Majalisun Dokokin Amurka

Majalisun dokokin Amurka sun tsayar da kudurin da ya basu damar yin nazari akan duk wata yarjejeniya da kasar ta cimma da kasar Iran akan shirin nukiliyarta

Majalisar Wakilan Amurka da gagarumin rinjaye ta amince da kudurin da zai baiwa majalisun dokokin Amurka damar amincewa ko akasin haka ga duk wata yarjejeniyar da Amurka da wasu manyan kasashen duniya zasu kulla da Iran.

A kuri'ar da aka kada jiya Alhamis wakilai dari hudu ne suka amince da dokar 25 kuma suka ki. Cikin makon jiya ne majalisar dattijai ta amince da kudurin inda wakilai 98 suka amince mutum daya ya ki. Fadar white ta shugaban Amurka tace shugaba Barack Obama, wanda da farko yayi barazanar hawan kujerar naki, yanzu ya sauya ra'ayi yace zai sanya hanu kan dokar.

Dokar zata baiwa majalisun dokokin biyu kwanaki 30 suyi nazarin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da Amurka da kuma wasu manyan kasashen duniya biyar.

A cikin kwanaki 30 din, dokar zata hana Mr. Obama janye takunkumi ko wani iri da Amurka ta kakabawa Iran.

Gwamnatin Obama ta nuna matukar adawa barin majalisun biyu su tsoma baki kan yarjejeniyar nukiliya da Iran, domin tana gudun hakan zai iya kawo kafar angulu a shawarwari da take yi da Iran.

Daga bisani Mr. Obama yayi barazanar hawan kujerar naki ganin 'yan jam'iyyarsa ta Democrat masu yawa suna goyon bayan kudurin, amma an sassauta wasu sharudda masu tsanani da aka kudura tun farko cikin dokar.

Karkashin yarjejeniyar Farisa zata amince ta rage karfin inganta sinadaran Uranium domin hakan zai hanata kera makaman nukiliya. Idan tayi haka kasashen yammacin duniya zasu janye takunkumin karya tattalin arziki wanda yayi mummunar illa ga tattalin arzikin Iran.

XS
SM
MD
LG