Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majinyata Sun Shiga Wani Hali Biyo Bayan Yajin Aikin Ma'aikatan Asibiti


Majinyata a asibitin kwararru a jahar Filato sun shiga hali mara dadi, bayan daukacin ma’aikatan dake asibitin, in banda likitoci, suka shiga yajin aiki na sai yadda hali yayi.

Ma’aikatan sun shiga yajin aikin ne don jan hankalin gwamnati ta biya su wadansu bukatunsu da suka jibanci albashi, alawus-alawus da kudaden adashen gata.

Wasu majinyata sun bayyana rashin jin dadinsu da yajin aikin, inda suka ce basu san inda zasu tafi ba, saboda basu da kudin zuwa asibitin kudi.

Shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin kwadago na asibitin, Mr. Ezekiel Makmang ya ce sun shiga yajin aikin ne saboda gwamnati ta kasa aiwatar da wadansu yarjejeniyoyi da suka amince.

Shugaban ma’aikatan jahar Filato bai maida amsar kira da sakon kar ta kwana da wakiliyar Muryar Amurka ta aike masa ba.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG