Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Kwashe Shekaru 120 Kafin A Sami Wadatar Likitocin Da Ake Nema A Najeriya -Ministan Ilimi


Adamu Adamu
Adamu Adamu

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa Najeriya za ta kwashe tsawon shekaru 120 kafin ta kai ga samun wadatattun likitocin da ake bukata a fannin kiwon lafiya, kuma sai idan likitocin sun ci gaba da zama a kasar ba tare da ficewa ba.

Minista Adamu Adamu ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsuwar fara karatun digiri karo na farko na jami’ar kimiyyar kiwon lafiya ta tarayya wato FUHSO, da aka gudanar a mazaunin jami’ar na wuccin gadi dake garin Otada na karamar hukumar Otukpo a jihar Binuwai.

Adamu ya ce jami’ar ta FUHSO da ke jihar Binuwai za ta cike gibin da ake samu na bukatar likitoci a Najeriya.

Ministan wanda ya sami wakilcin babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Sunny Echono, ya ce idan aka yi la'akari da adadin likitocin da ake yayewa a Najeriya a halin yanzu, kasar za ta kwashe kimanin shekaru 120 kafin ta samu adadin likitocin da take bukata a fannin kiwon lafiyarta, amma kuma sai idan likitocin da ke aiki a kasar sun ci gaba da aiki ba tare da fita kasashen waje aiki ba.

Haka kuma, Adamu ya ce kafa jami’ar FUHSO zai taimaka wajen kara horar da karin likitoci, gudanar da bincike da kirkire-kirkire don inganta tsarin kiwon lafiya da kuma kiyaye albarkatun kasa ta hanyar horarwa da bunkasa tattalin arziki a fannin ci gaban 'yan kasa.

Shi ma gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce yana alfahari da cewa jami’ar ta fara aiki gadan-gadan, ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta hada gwiwa da ma’aikatar lafiya ta tarayya domin tabbatar da ingancin karatru a jami’ar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Najeriya sun fara tofa albarkacin bakin su a game da kaddamar da aikin koyarwa a jami’ar inda wasu ke yabawa da samin ci gaban wasu kuma ke yin kira da gwamnati ta inganta yanayin aikin likitoci da walwalar su a kasar suna mai cewa maddin ba’a yi haka ba, likitoci zasu ci gaba da barin kasar don samun yanayin aiki mai kyau da albashi mai tsoka a kasashen da suka ci gaba.

Idan ana iya tunawa ma ko a cikin watan Satumba, likitoci da dama sun halarci wani wurin da ake neman aiki a kasashe larabawa da ma kasashen turai inda rahotanni suka yi nuni da cewa daga watan Mayun zuwa Satumba, likitoci sama da 350 sun bar kasar sun koma kasashen waje aiki.

Kusan duk shekara ana samin likitocin kasar suna gudanar da yajin aikin a bisa zargin rashin cika alkawura na biyan bukatun albashi da saura hakokki daga bangaren gwamnatin kasar.

XS
SM
MD
LG