Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makarantu 600 Aka Rufe A Arewacin Najeriya Saboda Masu Garkuwa Da Dalibai – Amnesty


Kujerun zama a makaranta dauke da sunayen daliban Chibok da aka sace. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Kalaman kungiyar na zuwa ne, yayin da aka cika shekara bakwai cif da sace ‘yan matan makarantar Chibok a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar.

Tsakanin watan Disambar 2020 zuwa watan Maris din bana, an yi garkuwa da dalibai akalla sau biyar a arewacin Najeriya, Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce.

Hakan ya sa aka rufe kusan makarantu 600 a yankin, Amnesty International ta ce a shafinta na Twitter a ranar Laraba, gudun kada a kai hare-hare a makarantun.

Kalaman kungiyar na zuwa ne, yayin da aka cika shekara bakwai cif da sace ‘yan matan makarantar Chibok a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar.

Wani mai zanga zanga dauke da kwalin neman a saki daliban Chibok a Najeriya
Wani mai zanga zanga dauke da kwalin neman a saki daliban Chibok a Najeriya

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014, mayakan Boko Haram suka sace daliban lamarin da ya janyo kakkausar suka a cikin da wajen Najeriyar.

“Yau shekara bakwai kenan da Boko Haram ta sace dalibai mata 279 a garin Chibok,” Amnesty ta ce a shafinta na @AmnestyNigeria.

Kungiyar ta ce, ko da yake, wasunsu sun tsere yayin da aka sako wasu, “amma har yanzu ana garkuwa da ragowar dalibai sama da 100.”

'Yar Majalisa Frederica S. Wilson a lokacin da ta gana da wasu daga cikin daliban Chibok da suka tsere a lokacin sace su
'Yar Majalisa Frederica S. Wilson a lokacin da ta gana da wasu daga cikin daliban Chibok da suka tsere a lokacin sace su

Amnesty ta kara da cewa fargabar sace dalibai a makarantunsu, ta sa an rufe makarantu da dama a yankin arewacin kasar.

“Duk irin matakin da gwamnatin ke dauka wajen ganin an shawo kan wannan lamari, ba ya aiki.”

Karin bayani akan: Chibok, Boko Haram, Amnesty International, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Dubun dubatar dalibai ba sa samun damar zuwa makaranta, saboda gazarawar da hukumomi suka yi wajen samar da tsaro a makarantu musamman a arewacin Najeriya.”

Hukumomin Najeriya dai sun sha nanata cewa suna iya bakin kokarinsu wajen samar da cikakken tsaro a makarantu musamman a arewacin kasar.

A lokacin da ya gana da dalibai 82 da aka sako daga cikin ‘yan matan na Chibok a watan Mayun shekarar 2017, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin ganin an sako sauran ‘yan matan da suka rage a hannun mayakan. Amma har yanzu babu duriyarsu.

Hotunan yadda aka tarbi daliban makarantar Jangebe a fadar gwamnatin jihar Zamfara bayan da aka sako su
Hotunan yadda aka tarbi daliban makarantar Jangebe a fadar gwamnatin jihar Zamfara bayan da aka sako su

A ‘yan tsakanin watannin da suka gabata, an sace dalibai a makarantun sakandare da ke Kankara a jihar Katsina, da daliban Jangebe da ke jihar Zamfara, sai na Kagara da ke jihar Neja da kuma daliban kwalejin nazarin harkokin kula da gandun daji da ke jihar Kaduna, dukkansu a arewacin Najeirya.

A mafi akasarin lokuta, akan biya kudaden fansa ne kafin a sako daliban, ko da yake, gwamnati ta sha musanta cewa tana biyan kudaden kafin a karbo daliban.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG