Accessibility links

Makarantun 'ya'yan makiyaya zasu sabbin littafai kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi alkawari

Gwanatin Najeriya ta yi alkawarin samarma makarantun makiyaya sabbin littafai a duk fadin kasar. Hukumar dake kula da makarantun ce ta bayyana hakan yayin da ta yi taro da malaman dake koyaswa a makarantun.

Mukaddashin sakataren hukumar Malam Ibrahim Yamsat ya ce a kokarinta na bunkasa ilimin 'ya'yan makiyaya da tabbatar da bada ilimin da ya dace, gwamnatin tarayya ta dauki wasu matakai. Jami'in ya kara da cewa tun da gwamnati zata bada kudin sayen littafai su a hukumance zasu rubuta littafai su hadasu wuri daya. Zasu yi na firamare da ma na sakandare yadda kowane dan 'makiyayi zai samu. Ya ce yin hakan cigaba ne.

Shi kuma Farfasa Mohammed Mahuta na Jami'ar Usmanu Dan Fodio ya ce matakin da gwamnatin tarayya ta dauka cigaba ne kuma abun yabawa ne. Ya ce gwamnati tana kokarin ta ga kowane yaro ko yarinya ya samu ilimi ba tare da la'akari da jinsi ba ko kabila. Ya ce lamarin yanzu lailai bai kamata a bar 'yan Fulani baya ba babu ilimi.

Malaman makarantun sun ce wannan abu da gwamnati ta dauki alkawarin yi ya karfafasu domin yaran da zasu koyas zasu samu littafai da zasu inganta iliminsu


Mustapha Nasiru Batsari bada karin mayani.
XS
SM
MD
LG