Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makon Gobe Za'a Fara Taro Da Majalisar Dinkin Duniya Take Yi Ko wace Shekara


Children wearing Halloween costumes recite the Pledge of Allegiance after becoming US citizens during a naturalization ceremony at the United States Citizenship and Immigration Services in Baltimore, Maryland.
Children wearing Halloween costumes recite the Pledge of Allegiance after becoming US citizens during a naturalization ceremony at the United States Citizenship and Immigration Services in Baltimore, Maryland.

Talata za'a fara taron da Majalisar Dinkin Duniya take yi duk shekara,inda shugabannin kasashen duniya daban daban suke halarta.

Majalisar Dinkin Duniya zata bude taron shekara shekara na bana ranar talata, a dai dai lokacinda ake ci gaba d a cacar baki tsakanin Amurka da Rasha, kan wanda za'a azawa alhakin kai hari da makamai masu guba a Syria. Hakanan kuma an fara ganin alamun Iran ta fara sassautowa daga tafarkin fito na fito da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyar d a ake zargin tana fakewa da shi ne domin habaka makaman nukiliya.

Parfessa Bube Namaiwa na jami'ar Anta-Diouf dake Senegal yace akwai alamun Majalisar zata fi maida hankali kan matakan sulhu a rikici iri daban daban da ake fama da su a fadin duniya.

Haka kuma shehin malamin ya yi magana kan kotun kasa da kasa da yadda tuhumar da ta yiwa shugaba Umar al-Bashir na Sudan ta janyo tankiya kan ziyarar da shugaban na Sudan yake so yayi zuwa New York domin ya halarci taron majalisar Dinkin Duniya, Amurka kuma tana sanyin jiki wajen bashi damar zuwa nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG