Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makusantan Shugaba Buhari Na Hana Mutane Ganinsa Ne Don Gudun Fada Masa Gaskiya - Dalung


Solomon Dalung
Solomon Dalung

Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya zargi wasu mukarraban shugaba muhammadu Buhari da yin katutu wajen hana mutane masu kyakyawar niyyar fadin gaskiya kan yanayin da kasa ke ciki ganinsa.

Solomon Dalung ya koka kan yadda wadanda suka fi kusanci da shugaban ke kange shi daga saduwa da masu kokarin ankarar da shi kan yanayin da kasa ke ciki na matsin tattalin arziki da ma yanayin tsaro don ba shi shawarar fitar da sabbin dabarun neman mafita kasa ta ci gaba kafin wa’adin mulkinsa ya kare a shekarar 2023.

A cewarsa, kusan kullum makusantan shugaban kan ba da uzurin karya kan cewa suna la’akari da cutar koronabirus ne don kare lafiyar shugaban, don haka shi ya sa ba da damar a iya ganawa da shi ba don dora shi kan turba ta gaskiya da aka san shi da da ita, da ma yi wa ’yan kasa hidima a matsayin sa na shugaban Najeriya.

Haka kuma, Dalung ya ce ya na da yakinin cewa mai yiwuwa wadanda ke hana mutane ganin shugaban kasa ba sa son a ba shi wata shawara a kan abin da yake faruwa musamman ta fuskar tabarbarewar tsaro saboda ta su manufa ta daban.

Buhari, hagu da Gwamna Matawalle, dama yayin wata ziyara da ya kai fadar shugaban kasar a watan Fabrairu (Twitter/Matawalle)
Buhari, hagu da Gwamna Matawalle, dama yayin wata ziyara da ya kai fadar shugaban kasar a watan Fabrairu (Twitter/Matawalle)

Kazalika, Dalung ya ce bai dace ba a ce ana hana mutanen da za su ba shugaban shawarar samun ci gaba, alhali kuma shugaban na halartar wasu taruka kuma ana barin sa karbar bakunci wasu mutane duk da cewa akwai cutar korona birus, amma kuma ana kange shi daga wasu masu fadan gaskiya don kar a tonawa wadanda su ke ba daidai ba asiri.

Mista Dalung dai ya yabawa kokarin shugaba Buhari kan yaki da matsalolin tsaro ya na mai cewa ba gazawa ne shugaban ya yi ba, illa dai a kara fitar da sabbin hanyoyin yaki da miyagun iri.

Ya kuma jaddada cewa idan shugaban na samun bayanan gaskiya game da yanayin da ake ciki da zai ninka kokain da yake.

Idan ana iya tunawa, a baya-bayan nan sai da gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci gwamnatocin jihohin arewa da ma shugaba Buhari su hada karfi waje guda don kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya.

XS
SM
MD
LG