Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Almundahana, EFCC Ta Gayyaci Tsohon Gwamnan Bayelsa Henry Dickson


EFCC
EFCC

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar Bayelsa ta Yamma Henry Dickson, ya musanta zargin wawure baitul malin jihar a yayin da yake kan kujerar gwamnan jihar.

Wata kungiya mai zaman kanta ce ta shigar da kara kan zargin Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa Henry Dickson, bisa zargin sama da fadi da kudaden gwamnati a shekaru 8 da yayi a matsayin gwamnan jihar.

Jami’an hukumar EFCC sun gayyaci tsohon gwamnan, inda suka yi masa tambayoyi a ofishin su da ke Abuja.

Dickson ya gabatar da kanshi a ofishin hukumar bayan da ya sami takardar gayyatar da aka aika masa bisa zargin barnata kudaden gwamnati da cin amanar aiki a tsawon shekaru 8 da yayi a matsayin gwamna tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2020.

A wata sanarwa a jiya Talata, Dickson ya ce ya bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta tanadar a lokuta da dama a ofishin hukumar da’ar ma'aikata ta Najeriya gabanin ya tsaya takarar gwamna.

Henry Dickson Gwamnan Jihar Bayelsa
Henry Dickson Gwamnan Jihar Bayelsa

Dickson ya kara da cewa “korafin ya danganci saka hannu jari da nayi a kamfanin iyalai na, wadda nayi rijistarsa a lokacin da nake majalisar wakilai a matsayin tanadin da nayi wa iyalai na tsakanin shekarun 1996 zuwa 2012 da na zama gwamna.

EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan ne bisa zargin wata kungiya mai zaman kanta da ba a bayyana sunanta, bisa zargin kin bayyana dukkanin kaddarorinsa, musamman ma gidaje da filaye a kauyensa na Orua a Yenegoa, da gidajen haya guda biyu a tarayyar Turai.

A bayanansa, tsohon gwamnan ya ce duk wadannan kaddarorin, ya mallake su ne ta hanyar rance da ya biya a hankali da kudaden albashinsa kuma ciki akwai guda da bai karasa biya ba kuma ya gabatarwa EFCC takardun.

Ya kuma jaddada cewa ya gabatarwa hukumar kula da da’ar ma'aikata takardun kaddarorin a lokacin da ya dace a shekara ta 2011, da lokacin takararsa ta gwamna a shekarun 2012, 2016, da 2020 da ya kamala aiki a matsayin gwamna sai kuma bana da ya bayyana kaddarorinsa a matsayin sanata.

Ya ci gaba da bayyana cewa yana biyan harajin da ya wajaba a kan sa da kamfanin.

XS
SM
MD
LG