Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malamai A Yankin Bamenda Suna Gudanar Da Zanga Zanga Yayin Da Ake Jarrabawa


Shugaban Kamaru- Paul Biya

Yayin da dalibai a kasar Kamaru suka fara rubuta jarabawar shekara shekara, jiya Litinin, daruruwan malaman su a yankin da ake amfani da harshen turancin Igilishi sun shiga tituna suna zanga zanga.

Malaman suna neman ingancin tsaro bayan da aka kashe takwarorin aikin su uku, aka kuma yi garkuwa da wani dalibi, banda wadanda aka sace ko kuma aka kashe a lokutan baya, da kona kaddarori a cikin shekaru biyu da ‘yan tawaye suka shafe suna tada kayar baya.

Malaman sanye da bakaken tufafi rike da kwalayen rubuta da suka bayyana bukatar tsaro, sun yi jerin gwano a wani titi dake garin Bamenda, babban birnin lardin arewa maso gabashin kasar.

Suka ce “Mun gaji, Allah ka taimaki malaman kasar Kamaru, ka taimaki malaman yankin arewa maso yamma. Bamu san abinda zamu yi ba. Bamu san inda zamu nufa ba.”

Malaman sun gudanar da zanga zangar jiya Litinin, a daidai lokacin da daruruwan daliban makarantar sakandaren Bamenda da ake koyarwa da harsunan Faransanci da kuma Turancin Ingilishi suke rubuta jarabawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG