Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Firaimare Sama Da 500 Suka Mutu A Rikicin Boko Haram A Borno - Comrade Muhammed


Gwamna Zulum a zauna a aji yana yi wa malamai jarabawa (Facebook/Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum a zauna a aji yana yi wa malamai jarabawa (Facebook/Gwamnatin Borno)

Majalisar Dinkin Duniya ta ware 5 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a duba halin da malamai suke ciki a sassan duniya.

Malamai 564 ne suka rasa rayukansu ko suka bata sanadiyyar rikicin Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban kungiyar makarantun Firaimare a jihar Borno Comrade Jibrin Muhammed ne ya bayyanawa Muryar Amurka hakan yayin da ake bikin tunawa da ranar Malamai ta duniya.

Hukumar raya al'adu da ilimi ta UNESCO a Majalisar Dinkin Duniya ta ware 5 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a duba halin da malamai ke ciki a sassan duniya da irin gudunmowar da suke bayarwa.

"Mu a Borno, adadin da muke da shi na malaman da muka rasa rayukansu da kuma wadanda aka dauke ko aka sace yau shekara 12, tun da aka fara rikicin har zuwa yau, muna da mutum 564." In ji Comrade Muhammed.

Rikicin Boko Haram ya halaka dubban mutane tun da ya faro a shekarar 2009 ya kuma raba miliyoyin da muhallansu.

Dangane da halin da iyalan malaman da suka mutusuke ciki, Comrade Muhammed ya ce kungiyar tana iya bakin kokarinta wajen ganin an tallafa musu duk da cewa rayuwa ta sauya a yau.

"Lamarin iyalai a yau gaskiya, wadanda mazansu ma suke nan a raye a wahala ake ballantana a ce uwa ta rasa mijinta an bar mata yara, ana cikin matsala."

Sai dai a cewar Comrade Muhammed, sun rubuta takardun koke zuwa wasu kungiyoyi domin a kai musu dauki, "kuma alhamdulillahi sun taimaka mana."

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:

Malamai Sama Da 500 Suka Mutu Sanadiyyar Rikicin Boko Haram A Borno - Comrade Muhammed - 3'19"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00


XS
SM
MD
LG