Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Jami’a Sun Yi Tsokaci Kan Zanga-Zangar Da Kungiyar Kwadago Zata Gudanar


Kungiyar ASUU
Kungiyar ASUU

Malaman jami’a a kudu maso gabashin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan zanga-zangar wuni biyu da kungiyar kwadago zata fara gudanarwa yau Talata don bai wa malaman jami’a hadin kai a yajin aikin da su ka kwashe kimanin wata shida suna yi kan gazawar gwamnatin wajen mutunta yarjejeniyarsu.     

A hirar shi da Muryar Amurka, Dakta Aloy Dimgba wani malamin jami’a na ganin tasirin wannan zanga-zangar, saboda zata karfafa kokarin da kungiyar malaman jami’a ke yi don ganin gwamnati ta mutunta yarjejeniyarta da ita.

Ya ce, “Wannan zai kara karfafa fafutukar da kungiyar malaman jami’a ke yi don sa gwamnati ta fara tattaunawa da ita da gaske, ko kuma ta mutunta yarjejeniyar da suka yi. Zanga-zangar zata sa duniya baki daya ta gane cewa gwamnati tana wasa ne da ita, kuma ya kamata a gaya mata abin da ya dace.”

A cewar Dakta Mohammed Auta da ke koyarwa a jami’ar Nnamdi Azikiwe a garin Awka, ya kamata a yi zanga-zangar don jama’a sun san cewa tura ta kai bango.

Sai dai Dakta John Onoh na jami’ar jihar Abia ya bukaci sanin irin zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kasa zata gudanar saboda idan har zanga-zangar kan titi kadai ne za a yi baza ta yi wani tasiri ba.

Ya ce, “ Shin har da dakatar da aiki gaba daya na tsawon wuni biyu za a yi ko tattaki akan titi kawai za a yi? Idan har zanga-zangar kan titi kawai ne za a yi, toh fa ina ganin baza ta yi wani tasiri ba. Amma idan har za a hada ne da dakatar da aiki a Najeriya gaba daya toh tabbas zata yi tasiri.”

Tun watan Fabrairun da ya wuce ne malaman jami’a a Najeriya suka shiga yajin aiki kan rikon sakainar kashin da kungiyar malaman ta ce gwamnatin tarayya ke yi wa bangaren ilimi, da kuma gazawar gwamnatin wajen mutunta wasu batutuwan da aka tada a yarjejeniyar gwamnati ta shiga da ita a shekarar 2009.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG