Kungiyar Malaman Makarantun Firaimare na Jamhuriyar Nijar ta SYNACEB, ta gudanar da wani taro a birnin Yamai, domin nazarin irin koma-baya da ilimi ya samu a wasu yankunan kasar da ke fama da matsalar tsaro.
Kungiyar ta kuma bai wa gwamnatin Nijar wa'adin mako guda domin biyan malaman kwantiragi albashinsu na watan Disamba.
A wata sanarwa da kungiyar ta SYNACEB ta fitar, ta nuna damuwarta game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da karuwa a wasu yankuna Nijar.
Wannan al’amari ya kuma jefa malaman makarantu da dama a cikin yanayi na damuwa musamman a yankunan Diffa, da Tillaberi, da kuma wasu garuwa da ke yankin Dosso.
A baya-bayan nan dai hukumomin yankunan Tillaberi da Dosso sun dauki mataki na haramta zirga-zirgar babura a wasu garuwa na yankunan, matakin da kungiyar ta SYNACEB ta ce, za su kara kawo cikas ga sha'anin koyarwa,
A wadannan yankuna, malaman makaranta ne suka fi yawon amfani da baburan idan za su je koyarwa.
Sai dai hukumomi yankunan da al'amarin ya shafa, na ci gaba da kare wadannan mataken tare da neman al’umma ta fahince su.
Saurari rahoto cikin sauti daga Yusuf Abdoulaye a birnin Yamai:
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 06, 2023
NIJAR: Yawan Matan Da Ke Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu.
Facebook Forum