Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ce Ta Fi Yawan Masu Ciwon Yoyon Fitsari A Duniya


Aikin gaggawa a asibiti
Aikin gaggawa a asibiti

Alakalumman wani bincike da aka yi sun nuna Najeriya ce ta fi kowace kasa a duk fadin duniya yawn mata dake kamuwa da cutar yoyon fitsari sanadiyar auren wuri

Najeriya ce kasar data fi ko wace a duk fadin duniya matan dake fama da cutar yoyon fitsari, domin ko an kiyasta cewa matan da yawan su yakai tsakanin dubu dari 4 zuwa dubu dari 8 suke dauke da wannan cutar da suke kamuwa da ita lokacin da suka zo haihuwa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace hanyar kadai da aka bi domin kamuwa da wannan cutar shine rage auren wuri, sai dai kuma maaikatan kiwon lafiya sunce al’adun jamaar kasar ma na ciki babban dalilin kamuwa da wannan cutar.

Wakiliyar wannan gidan Radiyon na sashen turanci Chika Oduah ta aiko muna da rahoto bayan ta ziyarci biranen Sokoto, Jos,da kaduna.

Inda ake da asibiti ko kuma sashe na musammam a asbitocin su da ake daukar dawainiyar yiwa masu wannan cutar magani kuma ta gana da wasu dake dauke da wannan cutar.

Asma’u Muhammadu wata ‘yar shekaru 12 ne da haihuwa kuma an yi mata auren fari a wannan shekarun yayin da takai shekaru 15 ta samu cikin ta na farko

“Lokacin dana fara nakuda ina son haihuwa nasha wahala sai da aka kaina asibiti, bayan na kwana 4 a ranar kwana na 4 ne na haihu amma yaron baizo da rai ba”.

Wannan wahalar data sha lokacin nakuda yasa ta samu yagewa a al’auran ta

Asmau tace tun daga wannan lokacin ta fahinci cewa ta fara wannan yoyon fitsarin.

Yanzu Asma’u takai shekaru 27 dahaihuwa amma har yanzu tana fama da wannan cutar na yoyon fitsari, haka ma mahaifiyar ta wannan shine ake kira da turanci Obsteric fistula.

Yanzu haka dai a Najeriya kusan matan da yawan su yakai rabin miliyan ne suke da wannan cutar ta Obsteric Fistula, musali Fatimatu Abubakar ‘yar shekaru 22 tace shekaran ta 4 tana fama da wannan cutar , abinda yasa mijin ya sake ta.

Mata da dama dake dauke da wannan cutar suna fuskantar mutuwar aure daga mazajen su wanda sau tari sai su zame tamkar wani abin zunde ko tsegumi cikin al’umma.

Dr Bello Lawal yace wani abu da mutane suka kasa ganewa shine al’adar yiwa masu wannan cutar aiki ko maganin gargajiya ba tare da sanin illar da hakan ke haifarwa na cutar ta yoyon fitsari ba.

Dr Bello Lawal yace jama’a cikin al’umma basu san babban abinda ke haifar da wannan cutar ba,yace akwai jahilcin dalilin abinda yasa ake kamuwa da wannan cutar, yace babban abu na farko shine tsawon dadewar mace tana nakuda, sai kuma yankan gishiri, wanda wanzamai keyi ko kuma yankan goriya duka wanzamai ne keyin sa yace wadannan sune abinda ke haifar da wannan cutar cikin dan kankanin lokaci.

Ilyasu Ningi dai wani wanzami ne wanda yake irin wannan yankan gishirin.

Yace wadannan kayayyakin da ake gani tare dashi sune kayan aikin sa na wannan yankan gishirin, yace yasan wannan aikin kwarai da gaske domin ko ya jima yana yinsa, yace yana iya bakin kokarinsa domin ganin cewa duk wanda yayi wa aiki an samu nasara kuma ana samu.

Yanzu haka dai akwai mata kusan dubu dari 2 a duk fadin tarayyar Najeriya da suke jiran ayi musu aikin wannan cutar na yoyon fitsari, saikuma inda matsalar take shine na rashin wadatattun likitocin da zasu yi wannan aikin, domin ko duk yawan wannan adadin likitocin basu wuce 12 da suke wannan aikin ba.

Idan muka koma ta kan Asmau ko wacce muka fara maganar ta da farko, ita kam ta rungumi kaddaran ci gaba da zama da wannan cutar.

“Tace bana jin dadi ko kadan amma yaya zanyi haka ALLAH ya kaddara rayuwa ta”

Yanzu haka dai a kalla mata dubu 20 a Najeriya ke kamuwa da wannan cutar a kowace shekara.

Ma'aikatan kiwon lafiya, ‘yan rajin kare hakkin bil’adama da jamiaangwamnati sunyi ittifakin cewa Najeria na da jan aiki gaban ta na ganinta kakkabe wannan cutar cikin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG