Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man City Ta  Lashe Gasar Premier


'Yan Wasan Manchester City.
'Yan Wasan Manchester City.

Manchester City ta zama zakarar gasar Premier, bayan da abokiyar hamayyarta Manchester United ta sha kaye a hannun Leicester City da ci 2-1 a ranar Talata.

Duk da cewa ta sha kaye a hannun Chelsea a karshen makon da ya gabata, City ta yi saurin farfadowa a wannan kakar wasa bayan da ta samu maki 12 daga wasa takwas da ta buga.

Kwallayen Caglar Soyuncu da Luke Thomas suka katsewa United hanzari, duk da kwallon da Mason Greenwood ya zura.

Yanzu City wacce ta ba da tazarar maki 10 a saman teburin gasar, na da wasanni uku da suka rage mata a wannan kakar wasa.

Hakan na nufin City, wacce ta jima tana jira ta fara bikin lashe kofin, ta lashe gasar a karo na uku kenan cikin shekara hudu da suka gabata.

‘Yan wasan na Pep Guardiola sun taka rawar gani a wannan kaka, abin da ya kara masu kwarin gwiwar kai wa ga gaci.

Wannan shi ne kofi na 10 da Guardiola ya samu tun bayan da ya samu tun bayan da ya je City a shekarar 2016

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG