Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester City Ta Kai Zagayen Semi-Finals a Gasar FA Cup


Karawar Manchester City da Leicester City a gasar Premier

Manchester City ta fara jin kamshin kofin gasar FA Cup, bayan da ta lallasa Everton da ci 0-2 a wasan da suka kara a zagayen Quarter Final.

Kwallayen Ilkay Gundogan da Kevin De Bruyne ne suka kai City ga gaci, wadanda aka zura su a bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a filin was ana Goodison Park.

A farkon wasan Everton ta kai wasu hare-hare da suka kara mata kwarin gwiwa amma har aka je hutun rabin lokaci babu wana ya samu zura kwallo a tsakanin kungiyoyin biyu.

Sauran minti shida a kammala wasan a lokacin da Gundogan ya shammaci Everton inda ya yi amfani da kansa wajen cin kwallon a ragar Everton.

Daga baya De Bruyne wanda ya shigo a matsayin dan canji a kurarren lokaci, ya doka kwallon cikin ragar Everton wacce ta kai wasan ci 0-2 dun da cewa ‘yan wasan na Everton sun kalubalanci cilla kafa da dan wasan City Riyad Mahrez ya yi kafin Bruyne ya ci kwallonsa.

Da yammacin Lahadin nan za a fitar da tsarin yadda kungiyoyin za su kara a zagayen na wasan kusa da na karshe - semi-finals a gasar ta FA Cup.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG