Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoma Shinkafa A Shimankar Jihar Filato Sun Koka


Wani yaro yake sussuka shinkafa a kauye
Wani yaro yake sussuka shinkafa a kauye

Al'ummar Shimankar dake jihar Filato sun bukaci gwamnati da ta gudanar da bincike kan kudinsu fiye da nera miliyan arba'in, kudin da suka ba gwamnatin tarayyar Najeriya shinkafa ta hannun wani kamfani mai suna TIDOL.

A jihar Filato akasarin mazauna garin Shimankar manoman shinkafa ne ko kuma masu sana'ar dake da alaka da shinkafa.

Ta bakin wadanda suka mika kokensu sunce shekaru da dama suna hulda da kamfanin ta hanyar basu ingantaccen iri daga gwamnatin tarayya. Bayan sun kammala noma da girbi kamfanin sai ya kwashe shinkafar da suka noma baki daya ya kuma biyasu cikin karamin lokaci.

Wadanda suka yi magana sun ce tun bara kamfanin ya karbi shinkafa kamar yadda ya saba yi amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa. Kudin da suka kai nera miliyan arba'in har yanzu ba amo ba kuruwa.

Wani Musa Aliyu Ibrahim yace sun kai shekara kusan ishirin suna harka. Sun fara ne da wani kamfanin gwamnatin tarayya National Seed. Daga baya gwamnati tace kamfanin TIDOL ne zai cigaba da yin harka dasu. Saidai kamfanin bashi da kudin biya sai ya dauki kayansu ya ba gwamnati idan an biyashi kana ya biyasu. Tun lokacin da suka kwashi kayansu bara babu wanda ya sake waiwayarsu.

Shugaban matasa na Shimankar yace tun watan daya na shekarar bara da suka kwashi kayansu basu sake dawowa ba.

Rashin biyansu ya hanasu noma a wannan shekarar.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG