Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoman Kamaru Na Korafin Hana Fitar Da Kayan Amfanin Gona Zuwa Najeriya


Cocoa
Cocoa

Kasar Kamaru na yaki da safarar koko da auduga da kuma sauran kayan amfanin gona zuwa Najeriya, inda ta haramta cinikaya na wucin gadi bisa ka’ida na tsawon dan wani lokaci.

Tun bayan sanar da haramcin makonni biyu da suka gabata, hukumomi sun aike da daruruwan 'yan sanda zuwa kan iyakar kasar inda suka kwace manyan motoci da dama.

Sai dai manoman Kamaru na zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da haramcin, suna masu cewa ya fi riba su sayar da kayayyakinsu ga Najeriya.

Jami’an ‘yan sandan Kamaru da jami’an kwastam sun ce sun tare dimbin manyan motoci da suka yi yunkurin safarar kayan amfanin gona cikin makonni biyu da suka gabata daga garuruwa da kauyukan arewacin kasar zuwa Najeriya.

‘Yan sanda sun ce sun kwace alkama da masara da shinkafa da koko da auduga tun bayan kaddamar da dokar hana fitar da amfanin gona na wucin gadi zuwa Najeriya a ranar 13 ga watan Yuni.

Koko (Cocoa) ne dai kashin bayan tattalin arzikin Kamaru
Koko (Cocoa) ne dai kashin bayan tattalin arzikin Kamaru

Ma'aikatar kasuwanci ta Kamaru ta ce ana bukatar haramcin ne saboda tana asarar dala miliyan 165 a kowace shekara daga safarar kayan amfanin gona zuwa makwabciyarta ta arewa – wato kashi 60% na jimillar cinikayyar.

Gwamnati ta umurci daruruwan 'yan sanda zuwa kan iyaka, ta kuma gano akalla manyan motoci 12 da suka tsere daga hannun hukuma.

Manoman Kamaru sun ce haramcin zai yi wuya a aiwatar da shi a kan iyaka mai tsayin kilomita 2,000.

Masu Noman Koko A Kamaru
Masu Noman Koko A Kamaru

Baba Ahmadou shi ne kakakin kungiyar manoman hatsi da ke kan iyakar arewacin Kamaru da Najeriya.

Da yake magana da muryar Amurka ta wayar tarho daga garin Mara da ke kan iyaka, ya ce manoma da yawa ba sa iya ajiyar amfanin gonakinsu domin su sayar a Kamaru.

Ahmadou ya ce Kamaru ba ta da isassun kayan aiki da za su kare koko da alkama da masara da shinkafa da dawa daga danshi da kura da kuma kwari da ke mamaye da lalata amfanin gona bayan girbi. Ya ce manoma sun gwammace su sayar da amfanin gonakinsu ga kasuwannin Najeriya, domin kayayyakin da ake sarrafa shinkafa, masara, da auduga sun tsufa, kuma ana dauke wutar lantarki akai-akai.

Masu Noman Koko A Kamaru
Masu Noman Koko A Kamaru

Ahmadou ya ce sayar wa ‘yan kasuwar Najeriya ma ya fi samun riba, kuma ya buga misali da cewa manoma za su iya samun karin kashi 20% na buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 da ba a sarrafa su ba.

Gwamnatin Kamaru ta yi korafin cewa tana biyan tallafin manoman don su sayar da amfanin gonakinsu a cikin gida akan farashin da aka amince da su.

Ministan kasuwanci na Kamaru Luc Magloire Mbarga Atangana ne ya sanar da dakatarwar.

Ya ce suna sane da kalubalen da gwamnati da manoma ke fuskanta.

Ma'aikatar Noma ta Kamaru ta ce fitar da koko ba bisa ka'ida ba zuwa Najeriya ya karu bayan da 'yan awaren masu Magana da harshen ingilishi a shekarar 2017 suka kaddamar da tawaye ga Yaoundé.

'Yan awaren Kamaru
'Yan awaren Kamaru

‘Yan tawayen dai na neman kafa kasar ‘yan aware daga kasar Kamaru mafi rinjayen masu magana da harshen Faransanci.

Shivron Arrey, wani mai fitar da koko a Kumba, wani garin da ke Kudu maso yammacin kasar da ke magana da Ingilishi, ta ce ‘yan tawayen sun hana su sayar da kayan amfanin gona ga garuruwan masu amfani da Faransanci.

"Yayin da ke cikin rikicin 'yan aware, kamfanoni ba sa zuwa sayen koko," in ji ta. 'Yan bindiga sun lalata motocin kamfanonin da ke yunkurin ciniki. Don haka, kasuwa mafi sauki da za su iya dogara da ita, ita ce ta kan iyaka a Najeriya.

Hukumomin kasar Kamaru sun ce sojoji na kare manoma daga ‘yan tawaye domin kasuwancin cikin gida ya dawo.

Sai dai manoman sun ce za a ci gaba da safarar ta barauniyar hanya zuwa Najeriya muddin zabinsu na fuskantar tashe-tashen hankula na ’yan aware da kuma rangwamen farashi a cikin gida ko kuma yin kasadar fitar da kayayyaki ba bisa ka’ida ba ta kan iyakokin kasar.

XS
SM
MD
LG