Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya Da Aka Rantsar Jiya Sun Sha Alwashin Maido Da Tsaro


Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya

Sababbin shugabanin hukumomin tsaro da Majalisar Dattawa Najeriya ta tantance sun yi alkawarin za a samu sauki a matsalar tsaro da ke addabar Kasar nan ba da jimawa ba.

Jim kadan bayan tantace shi da kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa suka yi, Shugaban Hafsoshin tsaron Najeriya, Manjo Janar Lucky Irabor ya bada tabbacin cewa kasar za ta samu saukin matsalar tsaro da ke addabar ta ya zuwa yanzu.

Janar Irabor ya ce zai tabbatar da hadin kai tsakanin ‘yan uwansa domin su sauya dabaru da zai kawo wa ‘yan kasa damar walwala a yanayi na zaman lafiya mai dorewa.

A makon da ya gabata ma dai majalisar wakilai ta tantance wadannan shugabanin kuma wannan shi ne karo na farko da za a tantance su har sau biyu a majalisar dokokin kasar, wani abu da shugaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako ya bada hujojji cewa kasa tana cikin halin kakanikayi saboda haka dole ne a tattauna, a bada shawarwari a bangarori daban daban, tare da ganin an hada kai wajen gudanar da aiki na kawo karshen rashin tsaro da kasa ta ke fama da shi.

Shi ma daya daga cikin 'ya'yan kwamitin da suka tantace jami'an, Sanata Bala Ibn Na'Allah ya ce ya gamsu da bayanan da jami'an tsaron suka bayar, inda ya nuna cewa in har an sama masu isassun kudade da kayan aiki, yana da yakinin za a samu nasara wajen shawo kan matsalar tsaron kasar.

Ranar 26 ga watan Janairun bana ne shugaba Mohammadu Buhari ya nada wadannan sababbin shugabanin hukumomin tsaron kasar su hudu, wadanda suka hada da Shugaban Hafsan Tsaron Kasar, Manjo Janar Lucky Irabor; da Babban Hafsan Hafsoshin Soja, Ibrahim Attahiru; da Shugaban Hafsan Sojojin Sama, Isiyaka Amao; da Shugaban sojojin Ruwa, Auwal Sambo.

A daidai lokacin da kwamitoci ke tantance sababbin Hafsoshin tsaron, a zauren Majalisar Dattawa kuma ana can an amince da tsofaffin jami'an a karkashin laftana Janar Yusuf Tukur Buratai a matsayin jakadu, wadanda ba na aiki ba wanda aka fi sani da Non Career Ambassadors a turance.

A saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya Da Aka Rantsar Jiya Sun Sha Alwashin Maido Da Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00


XS
SM
MD
LG