Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami'an Gwamnatin Najeriya Da Kamaru Sun Gana A Abuja


Khadija Bukar Abba Ibrahim, karamar ministar harkokin wajen Najeriya
Khadija Bukar Abba Ibrahim, karamar ministar harkokin wajen Najeriya

Manyan jami'an gwamnatin Najeriya da Kamaru sun gana a Abuja domin tattauna wasu muhimman batutuwan da kasashensu biyu ke fuskanta, musamman kasancewar 'yan gudun hijira da bakin haure da kuma ayyukan ta'addanci a iyakar kasashen biyu.

Karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, ta fadawa VOA cewa babban abinda aka sanya a gaba shi ne yadda za a tabbatar da tsaron iyaka mai tsawon gaske ta kasashen biyu. Ta ce karin kayan aiki da kayan tsaro sune zasu magance matsaloli na ta'addanci da fitintinun da ake fama da su a tsawon bakin iyakar kasashen biyu.

Shi kuwa Ministan tsare-tsaren iyakoki na kasar Kamaru, Emmanuel Rene Sady, ya jaddada muhimmancin daukar matakan da zasu tabbatar da tsaron kasashen biyu ta hanyar bin ka'idojin yarjejeniyar nan da suka rattaba ma hannu a tsakaninsu ranar 2 ga watan Maris na 2017 a birnin Yaounde a kasar Kamaru.

Ministan na Kamaru, ya ce, "tuni har wannan yarjejeniya ta taimaka mana wajen kara karfin tsaro a bakin iyakar kasashenmu, kamar yadda muke gani wajen yakar 'yan ta'addar Boko Haram da kuma dakile yin fashi cikin teku a yankin ruwan da ya hada kasashenmu."

Babban mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaron kasa, Mohammed Monguno, ya bayar da tabbacin cewa Najeriya zata taka rawa sosai musamman wajen samar da bayanan sirri da zasu kara tabbatar da tsaron iyakar kasashen biyu.

Ga cikakken rahoton Medina Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG