Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan jami'an tsaron Najeriya zasu bayyana gaban majalisaar dattawa kan 'yan matan Chibok


Sanata Bukola Saraki shugaban majalisar dattawan Najeriya

Jiya 'yan matan Chibok suka cika shekaru biyu cur a hannun 'yan Boko Haram da har yanzu babu duriyarsu ,dalili ke nan majalisar dattawan Najeriya ta bukaci manyan jami'an tsaro su bayyana gabanta su shaida mata kokarin da suka yi da kuma zasu yi domin kubuto da 'yan matan.

Majalisar ta umarci manyan jami'an tsaron ne da su shirya bayyana a zaurenta domin su bada bayanan kokarin ceto 'yan matan Chibok da yanzu suka cika shekaru biyu a hannun 'yan ta'adan Boko Haram.

Sanata Ibrahim Gobir dan majalisar yana ganin duk kokarin da aka yi ba'a yi nasara ba. Hanyar da za'a bi a ci nasara ita ce ta komawa kan binciken kwakwaf tare da taimakon kasashen waje irin su America, China da makamantansu. Idan ba'a nemi taimakonsu ba watakila ba za'a taba ganosu ba. Dalili ke nan da majalisar ta gayyaci manyan jami'an tsaro su ba majalisar shawara. Majalisar kuma zata so ta san inda aka kwana dangane da neman 'yan matan.

Amma majalisar wakilai nada kwarin gwuiwa za'a gano 'yan matan musamman bisa ga wani faifan bidiyo da CNN ya nuna inda aka fitar da hotunan 'yan mata su goma sha biyar da ake kyautata zaton suna cikin 'yan matan dari biyu da goma sha tara.

Haliru Dauda Jika dan majalisar wakilai yace gwamnati ta samu mafita akan lamarin abun da ya kamata a yi shi ne a cigaba da addu'a tare da karawa gwamnati karfin gwuiwan cigaba da yin anfanin kafar da aka samu na dawo da yaran.

Shi ma Garba Cede na majalisar wakilan ya ba gwamnati shawara akan iyayen 'yan matan. Yace a dinga ba iyayen tallafi na musamman maimakon kulawa da 'yan gudun hijira kawai. Kamata ya yi a bisu har gida ana taimaka masu tare da yi masu bayanai masu dadi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG