Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maganar ‘Yan Matan Chibok Ina Aka Kwana?


Nigeria Kidnapped Girls
Nigeria Kidnapped Girls

A farkon makon nan ne shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari ya ziyarci kasar Faransa, inda ya tattauna da wasu ‘yan Najeriya wanda ya shaida musu cewa suna tattaunawa da wasu ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram, don duba yiwuwar sako ‘yan matan nan da sukayi garkuwa da su na garin Chibok fiye da shekara guda kenan.

Wannan batu na shugaban kasa dai ya sake tayar da wata sabuwar muhawara, yayin da wasu ke ganin cewa wani abune mai wuyar gaske ace an sake samun wayannan mata kamar yadda suke, wasu kuma na cigaba da kyautata zato ne na cewa akwai yiwuwar sake gano wadannan ‘yan mata. Ko a makonni biyu da suka gabata ma sai da shugaban ya tura gwamnan jihar Borno Hon Kashim Shettima, don ganawa da iyayen matan na garin Chibok, inda ya shaida musu cewa nan bada dadewa ba gwamnati zata dawo musu da ‘ya ‘yan su.

Sanata Mohammed Ali Ddume ‘dan majalisa ne mai wakiltar mazabar kudancin Borno, wanda garin Chibok din ya zamanto karkashin sa bayyana ra’ayin sa kan wannan batu, inda yake ganin yanzu an sami shugaba da yake da gaske wajen ganin an samo ‘yan matan.

Wasu kuma iyayen ‘yan matan da aka sace sunce haryanzu dai suna jiran ‘ya ‘yan su kamar yadda shugaba yayi alkawarin za’a nemo su, suna kuma rokon Allah da yasa alkawarin da yayi na samo wadannan yara ya cika shi. Wasu iyayen kuma na fatan wannan alkawarin ba zai zamanto irin na shugabannin baya bane.

Wannan batu na ‘yan matan Chibok dai wani abune da duniya bazata manta ba, ganin yadda wadannan mahara suka kwashe yaran cikin dare ‘daya, kuma har ya zuwa rana mai kamar ta yau babu su babu duriyarsu, illa wadanda suka sami kubucewa tun a wancan lokacin.

Saurari rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG