Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin 'Yan Najeriya Kan Raba Kudin Da Abacha Ya Boye


Marigayi, Janar Sani Abacha
Marigayi, Janar Sani Abacha

'Yan Najeriya sun fara mayar da martani dangane da furucin gwamnatin kasar cewa, za ta fara raba Naira dubu biyar-biyar ga wasu ‘yan kasar da ke fama da talauci daga cikin kudade fiye da dala miliyan dari uku da ta ce ta karba a hannu hukumomin kasar Switzerland wadanda akace tsohon shugaban kasar Marigayi Sani Abacha ya boye a can.

Tuni dai gwamnatin ta ayyana wannan wata na Yuli a matsayin lokacin fara aiwatar da tsarin wadda matalauta dubu dari uku da biyu da 19 daga cikin jihohi 36 na kasar za su ci gajiyarsa.

Wasu 'yan Najeriya sun nuna ra'ayinsu kamar haka:

"Abin da ni ke gani kamar hirace gwamnati ta ke yi. Kamar ni din nan yanzu dai ka ga a wahalan ni ke, to in da gaske ne abin da aka fada to zan yi murna.To amma na san ba da gaske ba ne, a mayarwa wadanda ake ce sun sata kudinsu ya fi alkhairi ni a ra'ayina." inji Musa Lawal

Shi kuma wani Abubakar Umar cewa yayi,

"Ko da sun fito, to kudi nan fa gaskiya ba lallai ba ne su iso hannun talakawa ba. Ina da shakku akan haka saboda an dade ana zubda ruwa kasa ta na shanyewa."

Ko me kwararru ke fadi akan lamarin?

Wani masanin tattalin arziki a Kano, Dakta Lawal Habib Yahaya ya bayyana cewa wannan matakin ba zai yi tasiri ba domin a kasar da ke da yawan mutane na kusan sama da mutane miliyan 180, a ce ka dauki miliyan daya ka rage musu talauci, ba za a ji shi a kasar an rage talauci ba.

"Misali ka dauki durom na ruwa ka tafasashi da lipton ka dauki cokali daya na sukari ka zuba, ka zuba sukari amma babu wanda zai ce ka zuba. Don ko ka dandana ba za ka ji shi ba," inji shi

A cewarsa, idan aka yi la'akkari da manhaja na habbaka tattalin ariziki, kamata ya yi a dauki bangare daya kamar bangaren lafiya, misali a samu katon asibiti da talakawa suka fi amfani da shi, kamar asibitin Murtala da ke nan Kano.

"Idan ka ajiye dala miliyan goma ka zuba a wannan asibiti, to sai sun fi jinsa fiye da wannan dubu biyar-biyar din, kuma zai fi dorewa. Gwamnati ba za ta iya dorewa da bada kudi kurum ba tare da wani aiki ba," inji Dakta Lawal

Kungiyoyin rajin tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya su ma ba su gamsu ba da wannan aniya ta gwamnatin tarayya.

A wata sanawar kungiyar SERAP da mataimakin daraktan ta Timothy Adewale ya fitar a jiya lahadi, ta ce tsarin ba zai haifar da wani alfanu ga matalautan da aka ce za a zakulo domin cin gajiyar kudaden ba, a don haka kamata ya yi gwamnati ta sake tunani.

Ita ma dai kungiyar CISLAC ta soki wannan yunkuri tana mai bayyana shakku game da fa’idar wannan yunkuri na gwamnati na rarraba fiye da dala miliyan 300 a tsakanin matalauta ‘yan kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG