Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Doka A Amurka Sun Ce Trump Zai Iya Huskantar Matsalolin Shari'a


Shugaba Trump na Amurka
Shugaba Trump na Amurka

A kasar Amurka, ana fadin cewa babu wanda yafi karfin doka, koda kuwa shugaban kasa ne. To ko me ke faruwa ga shugaban kasa idan aka same shi da aikata laifi?

Wannan itace tambayar da ake ta yi a cikin wannan makon a Amurka, biyo bayan amincewa da aikata laifin take dokokin kudi na yakin neman zabe da tsohon lauyan shugaba Dopnald Trump, Michael Cohen ya yi, wanda yace ya aikata laifukan ne da umarnin dan takara na laokacin.

A wurin wani taron gangami a jihar Virginia ta Yamma a ranar Laraba, Trump ya yi watsi da wannan batun matsalolin shari’a, ya gana da magoya bayansa.

Trump yace a karkashin mulkin mu Amurka tana kara yin nasara kuma tana kara samun daraja a idon duniya. Amurka itace gaba da komai, yayin da jama’a suke Shewa.

Amma kuma amincewa da aikata laifi da Cohen ya yi da kuma hukuncin tabbatar da laifuka a kan tsohon manajan kyemfen Trump, Paul Manafort, ya baiwa jami’iyar Democrat wani sabon makamain siyasa da zata shiga zaben rabin wa’adin shugaban kasa da za a yi nan bada dadewa ba.

Shugaban 'yan Democrat a majalisar dattawa Chuck Schummer yace, idan abokai na daga bangaren Republican suka ja baki suka yi shuru a kan wannan batu, kenan hakan na nufin jami’iyarsu tana da hadin baki ga wannan dabi’ar rashawa da shugaban kasa ya dabibaye kansa dasu. Inji Schummer a wani jawabi da ya yi a zauren majalisar.

Masu fashin baki a kan harkokin doka sun fada a wannan mako cewa, akwai yiwuwar shugaba Trump yana da hannu a take dokokin kyemfe da Cohen ya amince da aikatawa kuma hakan zai iya jefa shugaban kasa cikin matsalolin shari’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG