Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masanan Afrika Sun Tattauna Bukatar Tantance Magani Na Kwarai


Wasu kwayoyin magunguna
Wasu kwayoyin magunguna

A yawancin kasashen Afirka baki daya, ana fama da kalubala a fannin wanda yake da hadarin gaske saboda sau da dama ba maida hankali sosai wajen tantance magunguna ko kuma kula da ingancin magungunan wanda ke kawo babban hatsari ga wadanda ke dogara gare su don samun lafiya.

A yawancin kasashen Afirka baki daya, ana fama da kalubala a fannin wanda yake da hadarin gaske saboda sau da dama ba maida hankali sosai wajen tantance magunguna ko kuma kula da ingancin magungunan wanda ke kawo babban hatsari ga wadanda ke dogara gare su don samun lafiya. Amma a karon farko wannan batun ya dauki hankalin shugabannin kasasheb nahiyar Afrika, wadanda ke yin taron ilimin kimiyya a Afrika ta kudu.

Samun magani mai lafiya zai iya yiwuwa a Afrika, inda ake samun kasuwar magunguna marasa kyau ko na jebu. Wannan na iya kawo babban hatsari inji Margaret Ndomondo-Sigonda yar kasar Tanzaniya wadda ke jagorantar wannan kungiya ta Afrika, wadda ke bada karfi wajen ganin cigaban nahiyar da ake kira NEPAD a takaice.

“Yawancin yanayin da kake gani a Afrika, shine yawancin magungunan dake a kasuwanninmu, fiye da kashi 30, ko dai basu kai matsayin inganci ba wanda ke nufin bazasu warkar da cutar da ake nufi ba, ko kuma na jebu ne, Wanda ke nufin ba na gaskiya bane,” inji Ndomondo Sigonda” shugabar ta bukaci sanin ko wannan na nufin basu da isassun kayan harhada magunguna ne yasa, basu sarrafa magunguna masu inganci a maimakon haka suke sayar da magunguna da zasu iya zama da hatsari ga marar lafiya mai makon warkar da cutar da ya kamata.

Ndomondo-Sigonda tana cikin masana dari da suka taru a Johannesburg domin taron kimiyya daya tara masanan lafiya, gwamnatoci da maaikatan lafiya domin tattauna yadda zasu tantance magunguna da kayan magani a dukan Afika.

Ndomondo-Sigonda tace yawancin kasashen Afrika basu da kwarewa a fannin harhada magunguna. Saboda haka kasashen suke nazarin hanyoyin gwaje gwajensu da nufin hada hannu da wadansu kasashen.

Masana kuma sun lura da kokarin da maaikatan tsaro zasu iya aiwatarwa wajen rage magunguna marasa inganci. Shi ma a nashi jawabin. shugaban ilimin kimiyya Aggrey Ambali yace hada hannu a wannan fannin zai taimaka wajen ganin an samar da magani da sauki ga masu saye.

Idan kasashe suka hada hannu tawajen gwajin magunguna, yace, zasu ajiye kudi. Kuma idan masu yin magani suka fahimci sabbin hanyoyi, zasu iya kwatantawa sosai.
Daga karshe. Ndomondo-Sigonda tace masu shan magani zasu iya kiyaye kansu yanzu ta wurin zabin inda zasu sayi magunguna da kuma tsayawa kan tabbatattun kayan aiki. Tace akwai hatsari duk lokacin da mutane suka je suka sayi magani a kasuwa, kawai ba wuraren da hukuma ta kayyade ba nan ne matsala ke farawa domin kaya a wannan kasuwanni, basu da tabbaci don ba’a san daga inda suke ba kuma kana iya sayen magunguna na jebu a kasuwan nin nan.

An nuna wannan a 2011, inda kungiyar lafiya ta duniya ta bayyana cewa a Nigeriya akwai babbar kasuwar magugunan jabu inda kusan kashi biyu bisa uku na yaki da cutar cizon sauro duk na jebu ne.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG