Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MASAR: Kotu ta Sake Dage Ranar Yankewa 'Yan Jarida na Al-Jazeera Hukunci


Wasu masu zanga-zangar neman a sako 'yan jarida a harabar kotun dake yi masu shari'a a kasar Masar
Wasu masu zanga-zangar neman a sako 'yan jarida a harabar kotun dake yi masu shari'a a kasar Masar

Kotu a Masar ta dage sauraren karar ‘yan jaridar gidan talbijin na Al Jazeera, wadanda ake tuhumarsu da nuna goyon baya ga kungiyar Muslim Brotherhood da aka haramta.

Alkalin kotun ya ce za a saurari matsayar ko kuma hukuncin da kotun za ta yanke a ranar 29 ga wannan wata na Agusta.

A baya an sa ran a ranar Alhamis da ta gabata ne za a yanke hukuncin, sai dai kotun ta yi ta dage karar, wacce ake tuhumar Mohammed Fahmy dan asalin kasar Canada da Baher Muhammed dan asalin kasar Masar da Peter Greste dan asalin kasar Australia wadanda aka tsare su tun a watan Disambar 2013.

Fiye da shekara guda wata kotun ta daban, ta ayyana ‘yan jaridar a matsayin masu laifi, inda ta yanke hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai akan Greste da Fahmy kana aka yankewa Mohammed shekaru goma.

Sai dai wata kotun daukaka kara ta ce a sake shari’ar bayan da masu shigar da kara suka gaza gabatar da kwararan hujjojin cewa sun nunawa kungiyar Muslim Brotherhood goyon baya.

Tuni dai aka sake Greste aka kuma mayar da shi Australia yayin da aka ba da belin Mohammed da Fahmy amma har yanzu suna nan a kasar ta Masar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG