Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Bincike Na Dab Da Gano Maganin Kwayar Cutar ZIKA


Kwayar Cutar ZIKA
Kwayar Cutar ZIKA

Jami’an kiyon lafiya masu gudanar da bincike sunce suna dab da gano maganin kwayar cutar cizon Sauron nan ta Zika wacce ka haifar da yawancin nakasa ga jinjirai tun suna cikin ciki uwar da ta kamu da wannan kwayar cutar a lokacin da take da juna biyu.

Wannan sabon maganin Zika da masu nazari a cibiyar kiwon lafiya ta kasar Amurka suka gwada kuma yana aiki, ya zama wani sabon nau’in magani ne wanda ke amfani da fasahar kwayar halitta ya karfafa garkuwan jikin mutum ta yadda zai iya yakar cutar.

Sakamakon yanda cutar Zika ke gaggauta yaduwa, nan bada dadewa ba za’a jarraba wannan magani. Izuwa yanzu ba a bada izinin jarraba wannan magani a kan bil adama ba a nan Amurka, amma dai dakin gwaji na Graham na kokarin kayyade yawan maganin da za’a rinka sha don samun cikakken kariya.

XS
SM
MD
LG