Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Keke-Napep Da Sojoji Suka Kai Mana Dauki - Wadanda Suka Tsira A Harin Filato


Gwamna Jihar filato.
Gwamna Jihar filato.

Wasu daga cikin matafiya da suka tsira da ransu a harin da wasu mazauna garin Jos ta jihar Filato suka kai musu, sun ce wasu masu tausayi a cikin al'ummar ne suka taimaka musu suka sami tsira da ran su a wannan harin.

Matafiyan kimanin 27 dai sun gamu da ajalinsu a lokacin da wasu mazauna Gada-Biyu a unguwar Rukuba dake karamar hukumar Jos ta arewa a jihar Filato suka tare motar da ke dauke da mutanen.

Mutanen na kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Ondo daga Bauchi, inda suka halarci wani taron addini.

Daya daga cikin wadanda suka tsira da ransu a harin, ya bayyana cewa masu tukin a daidaita sahu da jami’an soji ne suka kai musu agaji har suka sami damar tserewa daga hannun maharan da suka halaka wasu daga cikin abokan tafiyansu.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacinda ake samun karuwar adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadin mumunan harin na jihar Filato.

Rahotanni daga jihar Filato dai sun yi nuni da cewa matafiya 90 ne ke makare cikin motocin bus-bus 5, sa'adda maharan da ake zargin yan bindigan Irigwe ne suka afka musu.

Matafiyan dai sun halarci taron addu’a da aka saba gudanarwa na shekara-shekara a masalacin Dahiru Usman Bauchi don murnar zagayowar sabuwar shekarar addinin musulunci.

Wasu majiyoyi daga unguwar Rukuba sun ce rashin sani ya haifar da matafiyan suka bi wannan hanyar, a yayain da ake janaizar wasu mutanen garin da wasu batagari suka kashe.

Wasu da suka tsira da ransu, sun bayyana cewa a yayin da suka isa yankin Gada-Biyu, sun tarar da cunkoson ababen hawa kuma suka yi tsammanin cunkoso ne da aka saba fuskanta.

To amma ya ce kwatsam sai suka ga mutane da yawa daga kowanne gefen titin sun kewaye su tare da fara jifansu da duwatsu kuma ba bu yadda za su iya ficewa har aka fara karkashe wasunsu.

Haka kuma, jami’an tsaro sun sami nasarar kubutar da wasu mutane 36 daga cikin matafiyan.

Tuni dai aka sami yan Najeriya da kungiyoyi da dama suka yi Allah wadai da harin inda majalisar kolin harkokin addinin musulunci ta Najeriya, NSCIA karkashin jagoranci Sultan Sa’ad Abubakar, ta bayyana bakin cikin ta kan lamarin tare da tabbatar da cewa za’a dauki mataki kan lamarin.

Shi ma babban sufeta janar na yan sandan Najeriya, Usman Alkali-Baba ya ba da umarin tura jami’an tawagar shiga tsakani na gaggawa zuwa jihar Filato kai tsaye don kai dauki da duba lamarin da daukan matakan da suka dace don kawar da sake afkuwar irin wannan lamarin.

XS
SM
MD
LG