Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Kutse Na Rasha Sun Samu Nasarar Shiga Kundin Rajistar Masu Zabe A Wasu Jihohin Amurka


Wata babbar jami’ar Amurka mai kula da tsaron yanar gizo, ta fadawa gidan talabijin na NBC cewa masu kutse ko satar shiga yanar gizo daga Rasha sun sami nasarar shiga kundin rijistar masu zabe a wasu jihohin Amurka kafin zaben shugaban kasa na 2016.

Jeanette Manfra, shugabar sashen tsaron yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce Rasha ta auna jihohi 21, kuma kadan daga cikinsu an sami nasarar yiwa kutse.

Gidan talabijin na NBC ya ce ya tuntubi jihohin 21 da aka ce an auna. Biyar daga cikinsu da suka hada da jihohin Texas da California sunce su ba a kai musu hari ba.

Wannan abu da aka gano ya haddasa tsoro kan cewa Rasha ko wata gwamnati na iya sake yin katsalanda a harkokin zaben Amurka nan gaba, ta yin amfani da yanar gizo ko wasu dabaru na dabam.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG