Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Neman Shugabancin Amurka Sun Goyi Bayan Tsige Trump


Muwahawarar 'yan takarar jam'iyar Democrat
Muwahawarar 'yan takarar jam'iyar Democrat

‘Yan takarar shugaban kasar Amurka 7 da ke kan gaba na jam’iyyar Democrats sun tafka muhawara a daren jiya Alhamis, tare da caccakar shugaba Donald Trump da aka tsige, da suka bayyana a matsayin shugaba mafi gurbacewa a tarihin kasar.

Dukkan ‘yan takarar da ke neman ja’iyyar ta tsayar da su domin fafatawa da Trump a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa, sun ce suna goyon bayan matakin majalisar wakilai, na amincewa da daftarori 2 na zarge-zargen tsige Trump, saboda zargin sa da yin amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba domin amfanin kan sa a siyasance, da kuma kawo cikas ga zaman majalisa.

“Akwai bukatar mu dawo da martabar ofishin shugaban kasa” in ji tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Baiden, wanda shine ke kan gaba na yiwuwar samun kuri’un tsayar da shi takara a jam’iyyar ta Democrats.

Sen. Bernie Sanders wanda shi ne na 2 a bayan Baiden a kuri’un ra’ayoyin jama’a da dama, ya kira Trump “makaryaci” da ya sayar da al’ummar Amurka masu aiki.

‘Yan takarar sun ci gaba da maimaita caccakar Trump, duk da yake wasu lokuta sukan dawo caccakar junan su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG