Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ruwa da Tsaki a Najeriya Sun Dawo Daga Rakiyar Jonathan ke Nan?


Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan

Har yanzu wasikar da Obasanjo ya rubutawa shugaba Jonathan tana dada tada cecekuce in ma ba jijiyoyin wuyaba.

Mutane da yawa daga jihohi daban daban suna tofa albarkacin bakinsu kan wasikar da tsohon shugaban kasar Najeriya ya rubutawa Shugaba Goodluck Jonathan. Jihar Kano ma ba'a barta baya ba.

Dr. Saidu Ahmed Dokawa na sashen nazarin kimiyar siyasa na Jami'ar Bayero dake Kano ya yi bayani kan wasikar da kuma abun da zata haifar. Ya ce tsohon shugaba Obasanjo yana cikin rukuna hudu daga cikin rukuna biyar na Najeriya. Yana cikin sojoji da 'yansiyasa da attajirai da 'yantakarda. Wanda baya cikinsu shi ne na sarakunan gargajiya. Duka rukunan biyar a yanzu basa son wargajewar Najeriya. Akwai rukuni na shida wato alummar kasa da kasa ko kuma turawan yamma kuma Obasanjo ya yi bayani cewa mutane a ciki da wajen Najeriya basa jin dadin yadda Jonathan ke gudanar da gwamnatin Najeriya yanzu.

Dr Dokawa ya ce abun da za'a lura da shi a wasikar shi ne Obasanjo yana idar da sakon rukunin guda biyar ne. Sabo da haka a yanzu dukansu sun dawo daga rakiyar shugaba Jonathan. Don haka ba zasu yadda ya sake tsayawa takara ba. Idan kuma ya tsaya ba zai sake zama shugaban kasa ba a Najeriya. Wannan sauyin ne za'a samu a dalilin bayanan da Obasanjo ya bayar.

Alhaji Rabiu Abdullahi Garindanga mai sharhi kan alamuran siyasa kuma kantoman karamar hukumar Dala a Kano ya ce 'yan Najeriya suna son 'yan majalisun Najeriya lalle su bincika wannan al'amarin.Irin abubuwan da Obasanjo ya rubuta a cikin wasikar har da kashe mutane kaman dubu a ce 'yan majalisa basu sani ba basu yiwa 'yan Najeriya adalci ba.Hakin shugaban kasa ne ya kare rayukan 'yan Najeriya da kadarorinsu a ce kuma shi ne yake shirin hallakasu, yakamata a binciki lamarin. Haka kuma an zargeshi da daurewa cin hanci da rashawa gindi. An zargeshi da yin sakaci da harakar tsaro a kasar. Wadannan abubuwa sun isa majalisun kasar su bincika.

Mahmud Kwari nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG