Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Na Ganin Wulakanci Wajen Haihuwa A Afurka


Sakamakon wani bincike da aka buga a mujallar Journal The Lancet da ke mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi fannin kiwon lafiya, ya nuna sama da sulusi (ko kashi daya daga cikin kashi uku) na mata, a wasu kasashe hudu, sun fuskanci tsangwama da cin zarafi yayin da suka je haihuwa.

Nazarin, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta gudanar a Ghana, Guinea, Myanmar da Najeriya, ya gano cewa kashi 42 cikin dari na mata kan fuskanci wulakanci da ya hada da duka da zagi ko nuna wariya, yayin da su ka je haihuwa a asibiti.

Daga cikin mata dubu-biyu-da-sha-shida da aka gudanar da bincike akansu, kashi 14, sun ce an dake su ko an mare su yayin da suke haihuwa, yayin da kashi 38, suka ce, an zage su ko an tsawata masu tare da kunyata su, yayin da su ke haihuwa.

Binciken har ila yau, ya gano cewa, akan yi wa mata da dama aiki (ko tiyata) domin a cire jariri, ko a gudanar da gwaje-gwaje a al’aurarsu, ba tare da an nemi izininsu ba, sannan kashi 75 sun ce an kara musu fadin dubura yayin da su ke haihuwa ba tare da an nemi izninsu ba.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG