Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Donald Trump, Mike Pence Ya Kareshi


Mike Pence da Donald Trump
Mike Pence da Donald Trump

Biyo bayan kalamun dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump ya yi akan Mr. Khan wanda ya kalubaleshi da ya jawo cecekuce, mataimakinsa ya fito ya kareshi da cewa dan Khan wanda soja ne ya mutu a matsayin jarumi ne.

Mutumin da zai tsaya a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin jam’iyar Republican a zaben shugaban a kasar Amurka, Mike Pence, ya ce shi da abokin takararsa, wato Donald Trump, sun yi amannar cewa sojan kasar nan Musulmi da ya mutu a Iraqi a wani harin kunar bakin wake a shekarar 2004, ya mutu a matsayin jarumi.

‘Yan takarar biyu sun kuma kara da cewa, ya kamata kowane ba’Amurke ya yi alfahari da iyalan irin wadannan sojoji.

Trump da Pence sun fitar da wannan sanarwa ce, bayan da mahaifan Kyaftin Humayun Khan suka bayyana a babban taron Democrat a makon da ya gabata.

A sanarawa da suka fitar, Pence ya caccaki shugaba Barack Obama da ‘yar takarar jam’iyar Democrat Hillary Clinton da daukan matakan da suka bari kungiyar ISIS ta tsunduma cikin rikicin yankin Gabas Tsakiya.

A shekarar 2002 Pence da Clinton sun kada kuri’ar amincewa da kaiwa Iraqi hari a lokacin suna ‘yan majalisar dokoki.

XS
SM
MD
LG