Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya yanke shawarar ba zai shiga takarar neman jam'iyyar sa ta Democrat ta tsaida shi takarar shugabancin Amurka ba. Mataki ya kawo karshen jita-jitar ko zai yi takarar ko kuma a'a.
Da yake magana jiya Laraba a fadar White House, Mr. Biden yace har yanzu shi da iyalinsa suna juyayin mutuwar dansa Beau wandaAllah Ya yiwa rasuwa cikin watan Mayu, bayan da ya kamu da cutar kansa.
Mr. Biden yace kodashike ba zai yi takara ba, duk da haka zai ci gaba da magana sosai kan alkiblar da ta kamata kasar ta dosa.
Ya kuma yabawa shugaba Obama yana cewa "ya shugabanci Amurka cikin mawuyacin hali, har gashi yanzu ta farfado.