Accessibility links

An sake maido da matakan tsaron da aka takaita lokacin azumi a Gombe

Ana gap da kama azumi gwamnatin jihar Gombe ta janye dokar hana zirga-zirga da babura musamman wadanda ake anfani da su wurin daukar fasinjoji.

Kamar gwamnati ta manta da dokar sai gashi kwatsam gwamnatin ta dawo da dokar. Ta bakin DSP Faje Attajiri dokar ba wai an cireta ba ne gaba daya. An yi hakan ne domin musulmai su samu su yi azumi cikin walwala su kuma samu suna zuwa karatu ko tafsiri. Da aka fada masa cewa dawo da dokar kamar ba'a samu zaman lafiya ba ke nan sai ya ce komi suka yi domin a samu zaman lafiya ne. Dokar zata fara aiki daga karfe biyar na yamma zuwa karfe shida na safe. Wanda ya karya dokar za'a gurfanar da shi gaban sharia.

To sai dai dawo da dokar ta samu tofin alatsine daga mutanen garin Gombe. Sun ce basu ga dalilin da zai sa a dawo da dokar ba. Dimokradiya a ke yi. Abun da gwamnati ta yi ba dimokradiya ba ne. Sun ce zalunci ne gwamnatin ta yiwa al'ummar garin. Suka ce dawo da dokar ba karamin masifa ba ne zai jawo wa mutane. In jisu an dawo da dokar ne a farantawa wasu rai.

Dokar ta fi shafar 'yan acaba. Sun ce ba'a kyautatamasu ba. Rashin adalci aka yi masu domin abu ne da ya shafi talakawa domin zai kawo masu kuncin rayuwa.Wani dan acaba nada 'ya'ya goma da mata biyu kuma da sana'ar acaba yake ciyar dasu. Yanzu dokar ta tauye masa hakinsa.

Dokar ta samo asali ne bayan da wasu 'yan bindiga kan babura suka harbe wani dan majalisa a garin Gombe. Sai dai masu fashin baki sun ce dawo da dokar ba zai haifi da mai ido ba illa ta kara talauci da kuncin rayuwa da rashin aikin yi wadanda ka iya haddasa tashin hankali.

Abdulwahab nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG