Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Sun Kashe Manyan Mutane A Bauchi


Wasu 'yanbindiga

Wasu 'yanbindiga su hudu sanye da rigar soji sun harbe manyan mutane hudu a Bauchi

Rahotanni dake fitowa daga jihar Bauchi sun ce wasu 'yanbindiga hudu sanye da rigunan soji sun harbe shugaban asibitin gwamnatin tarayya dake garin Azare Dr. Musa Mohammed Dambam kana suka je fadar hakimin Dambam din suka kashe shi.

Da yake kara haske game da lamarin kwamishanan 'yansandan jihar Bauchi Alhaji Mohammed Ladan ya ce daidai wajejen karfe goma da rabi daren jiya wasu mutane hudu sanye da rigunan soji suka isa fadar hakimin suka kwace wayar hannunsa da wasu abubuwa kana suka kasheshi. To amma kafin su isa fadar sun tare Dr Musa Mohammed Dambai suka kwace motarsa kirar Toyota Camry baka suka kuma kasheshi. Da motarsa suka isa fadar hakimin.

Yayin da 'yansanda suka ce suna kan binciken ko su wanene suka yi aika-aikar su kuma mutanen garin Damban sun shiga rudani. Lamarin ya kadasu sosai yadda kowa sai kuka yake yi. Likitan da aka kashe da hakimin 'yan'uwan juna ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG