Accessibility links

Matan Filato Sun Bi Sawun Masu Gangami Akan Cibok


Matan Filato sanye da bakaken kaya

Zanga-zanga akan daliban Chibok da aka sace ta zama ruwan dare gama gari mkama daga arewa zuwa kudancin Najeriya inda yanzu ma matan Filato a tsakiyar kasar sun bi sawun takwarorinsu

Kungiyoyin mata na Musulmai da na Kirista sun bi sawun takwarorinsu mata a jihohin Najeriya sun shiga zanga-zangar neman a sako ko a kubuto da dalibai mata da aka sace daga Chibok.

Kungiyoyin matan da suka yi zanga-zangar sun isar da sakonsu wa gwamnati inda suka bukaci a yi duk abun da za'a iya yi a kubuto da yaran da aka sace a garin Chibok dake jihar Borno da kuma dakile matsalolin tsaro a kasar.

Matan sanye da bakaken kaya Musulmi da Kirista sun yi kuka a fadar gwamnati suna dauke da sakonni daban daban da suka rubuta a kwalaye wadanda suka hada da a dawo masu da 'yan matansu a kuma inganta tsaron rayuka da dukiyoyi. Sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsare iyaka ta kuma hada hannu da kasashen Chadi da Niger da Kamaru da kuma hukunta masu ta'adanci da dai sauransu.

Madam Esther Ibanga shugaban mata bangaren Kiristoci tace abun da suke gani yanzu a Najeriya mata sun zama "gidajen yaki" domin a kowane addini ko dokokin kasa da kasa a yaki ba'a taba mata. Dalili ke na suka bukaci gwamnat ta tashi ta tabbatar cewa mata da 'yan mata ba'a taba su ba. Tace yanzu a Najeriya babu inda mutum zai je ya kwanta cikin kwanciyar hankali. Tace da can baya lokacin rigingimun jihar Filato mata sun fito karara sun ce matsalar Filato na iya shafar kasar gaba daya. Sabili da haka a tashi a taimakawa jami'an tsaro da labaru masu mahimmanci.

Hajiya Khadija Gambo Hawaja shugabar mata bangaren Musulmai tace hakkin gwamnati ne ta kare 'yan kasa. Tace sun zo ne su gayawa gwamnati ta farka idan barci ta keyi. Yakin da a keyi yanzu ya shafi Musulmi da Kirista. Tace a shirye suke a matsayinsu na 'yan kasa su taimaka domin gwamnati ba zata iya yi ita kadai ba. Sun fito su gayawa duniya cewa shugaban kungiyar Boko Haram ba addinin Musulunci ya keyi ba ko kuma yake fada ba. Abubuwan da su keyi sun sabawa Kur'ani da koyaswar Manzon Allah. Tace maganganunsa zagi ne ga addinin Musulunci. Ya zama wajibi Musulmai su fito su nuna wannan ba addininsu ba ne. Yana yaki ne da Allah kuma Allah baya barci.

Daga yanzu sun dinga damun gwamnati ke nan akan Shekau. Shin wai shi wanene, kuma su wanene suke daure mashi gindi. Shin wai ina ne yake samun kudade. Ina ne yake boye mutane. Tace a shirye suke su goyi bayan kama duk munafukan dake taimaka masu da kowane irin abu. Kayan sojoji da 'yan kungiyar ke sanyawa ina suka samesu.

Gwamnan jihar Filato ya yabawa matan akan yadda suka nuna juyayinsu. Ya kara da cewa gwamnati da jami'an tsaro suna kokari wajen dawo da 'yan matan. Daga karshe matan sun yi addu'o'in kawo zaman lafiya a Najeriya.

Ga rahoton Zainab Babaji.
XS
SM
MD
LG