Matan dake zaman dirshen sun taru ne a harabar ma'aikatar ministar cigaban mata dake Yamai fadar gwamnatin Nijar.
Suna zaman dirshen din ne domin nuna fushinsu dangane da kason da gwamnati ta basu a cikin sabuwar gwamnatin da shugaban kasa Mahammadou Issoufou ya kafa.
Daga cikin ministoci arba'in da ukku da gwamnatin ta nada mata takwas ke cikinsu ko kaso bakwai cikin dari maimakon kaso 25 da doka ta tanada da ya kamata a ba mata.
Alkalummar kidigdiga sun bayyana cewa fiye da rabin al'ummar kasar mata ne saboda haka kungiyoyin matan suka ce da sake, wai an ba mai kaza kai, inji shugabar hadin gwiuwar kungiyoyin mata Madam Tako Hajiya Fatima.
Shugabar ta kira gwamnati ta daidaita sahu ta fuskar mukaman gwamnati da duk fannonin kasar ta yadda za'a sa mata a wuraren da suka kamata saboda akwai mata masu ilimi daban daban, inji Madam Fatima.
Madam Fatima tace sun jawo hankalin gwamnatin akan abun da kundun tsarin mulki ya fada saboda ba mata ba ne suka rubuta kundun ba. Tace wajibi ne su kiyaye da abun da kundun tsarin mulki ya fada ya kuma halartar.
Rashin wani hobasan mata cikin jam'iyyun siyasa na cikin dalilan da suka sa ba'a basu kason da ya dace ba, lamarin da kan mayar dasu 'yan kallon baya a harkokin gwamnati..
Saidai Madam Haruna Aisha Fatima wata 'yar siyasa na cewa lamarin ba haka yake ba. Tace jam'iyyun siyasa ne basa bada sunayen mata. Inji Fatima shi shugaban kasa da ya dauki rantsuwa a gaban jama'a ya kare kundun tsarin mulkin kasar ya kamata ya jawo hankalin 'yan siyasa kafin ma su gabatar da sunyaen ministoci.
Lokacin da take karbar wasikar korafinsu da suka gabatar mata, ministar cigaban mata Madam El-Bak Zainabu cewa tayi "idan an mikawa Firayim Ministan kasar sunayen da basu kumshi mata ba cewa yake a mayar, ke nan matsalar ba ta gwamnati ba ce, ta 'yan siyasa ce"
Da yake bayyana ra'ayinsa kan korafe korafen matan Abdu Idi wani jami'in fafutika na ganin lokacin soke dokar dake tanadin wani kaso ma mata ya zo. A tashi fahimtar tsarin baya anfanan matan karkara.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.