Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar da Aka Kona a Bauchi Ba 'Yar Kunar Bakin Wake Ba Ce


Janaral Buhari a Bauchi, Janairu 31, 2015.

Matar da ta gamu da ajalinta a Bauchi ba 'yar kunar bakin wake ba ce tabuwar hankali gareta.

Hukumar 'yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa matar da aka kona akan zargin cewa 'yar kunar bakin wake ce ba haka ba ne. Ba 'yar kunar bakin wake ba ce.

An tabbatar cewa matar da ta gamu da ajalinta ranar Lahadin da ta gabata tana fama da tabuwar hankali ne. Binciken da aka yi ya nuna cewa babu wani abu mai kama da bom ko makamanninsa a jikinta.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Haruna Muhammad shi ya bayyana hakan. Yace mutanensu dake warware bamabamai sun zagaya, sun duba, sun bincika amma babu wani abu mai kama da bom ko wani abun dake da alaka dashi. Yace bisa ga alamu mutane sun bi jita-jita ne sun hallakata.

Iyayen matar sun tabbatar da cewa 'yarsu ta sha fama da tabuwar hankali. Duk lokacin da ya kammata sai tayi fashe-fashe. Ranar da ta bar gida sai da tayi fashe-fashe kafin ta fita. Yayin da ta bar gidansu babu wanda ya san lokacin.

Kawun matar Tabitha yace taya akan sa mata kana aka cinna mata wuta. Yace Tabitha tana fama da tabuwar hankali kuma an sha kaita asibiti sashen dake kula da masu tabuwar kai. Yace tun ranar Asabar da ta fita suke ta cigiyarta. Suna cikin nemanta aka kawo masu rahoton cewa an kasheta sabili da ana zaton 'yar kunar bakin wake ce.

Ga karin bayani daga Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG