Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Kona Hedikwatar 'Yan Sanda Da Wani Dan Bindiga


Konannen ofishin yan sanda.

Lamarin rashin tsaro a arewacin Najeriya na ci gaba da daukar sabon salo, inda jama'a ke nuna bukatar daukarwa kan su hukunci.

Irin hakan ya faru a jihar Sakkwato dake arewacin kasar inda matasa suka husata suka kona ofishin ‘yan sanda da wani da ake tuhumar dan bindiga ne, saboda an hana su daukar doka a hannun su.

Ofishin Yana sanda da aka kona
Ofishin Yana sanda da aka kona

Da safiyar ranar talata ne wasu da ake tuhumar ‘yan bindiga ne suka shiga wani kauye mai suna Kainuwa su ka yi fashi gidan wani Alhaji, inda bayan sun wuce jama'ar garin suka bi sawun su, suka tarar da wasu mutane 6 suka kama su akan tuhumar su ne barayin.

Daga nan suka hannun ta su ga jami'an ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.

Rundunar 'yan sanda ta jihar ta bakin kakakin ta ASP Sanusi Abubakar tace bayan da DPO ya karbi mutanen sai jama'ar suka nuna bukatar a basu su su kashe.

Karin bayani akan: ASP, Sanusi Abubakar, ‘yan bindiga, jihar Sakkwato, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Wannan na zuwa ne lokacin da wasu al'ummomi ke ta fuskantar hare-haren ‘yan ta'adda musamman a gabascin Sakkwato duk da watan azumi da ake ciki.

Bisa ga yadda jama'a ke kokawa akan ayukkan ta'addanci da ke salwantar da rayukan da dukiyoyi, rashin samar da hanyoyin magance wannan matsalar kan iya haifar da wasu matsaloli a nan gaba kamar yadda alamu suka nuna na jama'a na son a bari su kashe yan ta'adda da kan su.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Dubi ra’ayoyi

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG