Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan gudun Hijira Na Neman A Sama Musu Muhalli Yayin Da Gwamnatin Borno Ke Shirin Rufe Sansanoni


Wasu 'yan gudun hijira a jihar Bornon Najeriya (Facebook/ Borno Government)
Wasu 'yan gudun hijira a jihar Bornon Najeriya (Facebook/ Borno Government)

Rahotanni daga jihar Borno sun yi nuni da cewa akasarin ‘yan gudun hijirar da ke zama a sansanin Bakassi sun bayyana aniyarsu ta komawa gida da kuma komawa gudanar da ayyukan noma domin samun abin dogaro da kai maimakon dogaro da dan kankanin kayan agaji da ake ba su.

Sai dai akasarinsu sun nuna damuwarsu kan makomar ’ya’yansu, wadanda ke karatu a manyan makarantu a Maiduguri ba tare da wuraren kwana ba.

A baya-bayan nan ne gwamnatin jihar Borno ta bayyana shirinta na rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira a karshen wannan shekara sakamakon dawo da zaman lafiya a yankuna da dama da mayakan na Boko Haram suka mamaye a baya.

A ranar asabar da ta gabata ne gwamna Babagana Umara Zulum, na jihar Borno ya ziyarci ‘yan gudun hijira na sansanin Bakassi, inda ya shaida wa mazauna sansanin cewa za'a rufe sansanin, kuma za a ba su tallafin da suka dace don komawa gida.

Idan ana iya tunawa a watan Mayu ne gwamnati ta rufe sansanin 'yan gudun hijirar dake kwalejin karanatar da addinin Islama da nazarin shari'a na Mohammed Goni don ci gaba da ayyukan ilimi da aka saba a da.

‘Yan gudun hijira daga kananan hukumomin Marte, Gwoza, Monguno da kuma Guzamala sun kwashe shekaru bakwai suna zaune a sansanin Bakassi sakamakon rikicin mayakan Boko Haram wadanda akasarin garuruwan su mutane sun kaurace mu su sakamakon yadda mayakan Boko Haram suka lalata su gaba daya da hare-hare.

Shugabar matan ’yan gudun hijirar daga karamar hukumar Gwoza a sansanin Bakassi, Hauwa Amadu, ta yi maraba da matakin da gwamnati ta dauka na tallafa wa ‘yan gudun hijirar na komawa gida tare da yaba wa gwamna Zullum kan yadda ya ba wa walwalar iyalai da suka tsinci kan su cikin mawuyacin hali mahimmanci kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Hauwa ta ce galibin iyalan da suka rasa matsugunansu suna zaune a sansanin ne sakamakon yadda ba su da wani zabin illa su zauna, kuma kokarin ba su matsuguni na kan su wato na dindindin zai kara musu damar dogaro da kai.

A cewar Hauwa, baya ga garuruwan Gwoza, Pulka, Izge da wasu ‘yan garuruwan, yawancin kauyukan da ke karkashin karamar hukumar Gwoza sun zama ba kowa a ciki, wanda hakan ya nuna dalilin da ya sa mutanen Amagda, Guduf, Kuranabasa, Wala, Dure da Gasha ke zama a cikin wasu al’ummomi daban.

Kazalika, Hauwa ta ce shirin da hukumomin jihar suka yi na aike da ‘yan gudun hijira da dama daga karamar hukumar Gwoza da ke zaune a Maiduguri zuwa Limankara mataki ne da ya dace matukar dai an samu isasshen wurin kwana da tsaro.

Hauwa ta yi kira ga gwamna Zullum da ya tabbatar an samar da isassun gidaje da wuraren ilimi kafin a sake tsugunar da mutane a kowane wuri.

Hakazalika, shugabar matan ’yan gudun hijira daga karamar hukumar Guzamala a sansanin Bakassi, Hajja Gumsu ta ce garinsu Gudumbali hedkwatar karamar hukumarsu da kuma matsugunan da ke makwabtaka da su ba sa iya zuwa inda ta roki gwamnati da ta samar da wani tsarin bada urin zama ga ‘yan gudun hijirar kafin a rufe sansanin Bakassi.

Hajja Gumsu ta ce yawancin iyalan da suka rasa matsugunansu sun shirya tsaf don a sake tsugunar da su a wurare masu aminci da kuma tabbatar da bukatun rayuwa.

Haka kuma shugaban ‘yan gudun hijira daga karamar hukumar Monguno a sansanin Bakassi, Alhaji Abatcha Baichu, ya ce a shirye yake ya koma gida da iyalansa amma mayakan Boko Haram sun lalata masa gidansa da ke garin Monguno.

Abatcha ya ce akwai ‘yan gudun hijira dubu 9 da 845 daga karamar hukumarsa a sansanin Bakassi inda su ke jiran umarnin gwamna na komawa wasu wurare.

Wani babban jami’i a hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa ya ce jimillar yawan ‘yan gudun hijirar da ke sansanoni ‘yan gudun hijira a jihar Borno 245 da iyalai dubu 190 da 591 wadanda sun kunshi mutane dubu 831 da 321.

XS
SM
MD
LG